'Yan Bindiga Sun Ga Takansu Yayin da Suka Yi Yunƙurin Kai Farmaki a Jihar Kaduna
- Dakarun rundunar sojojin Najeriya sun halaka ɗan bindiga a yankin ƙaramar hukumar Birnin Gwari da ke jihar Kaduna
- Gwarazan sojojin sun yi musayar wuta da ƴan bindigar ne yayin da suke hanyar zuwa kai hari kan mutanen da ba su ji ba kuma ba su gani ba
- A cewar rundunar sojin yanzu haka jami'ai sun bi bayan maharan da nufin kamo su domin su girbi abin da suka shuka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kaduna - Jami'an rundunar sojojin Najeriya sun kashe ɗan bindiga ɗaya yayin da suke hanyar zuwa kai hari a titin Birnin Gwari a jihar Kaduna.
Tawagar miyagun ƴan bindigar sun fito da nufin zuwa kai hari, kwatsam sojoji suka masu kwantan ɓauna suka hallaka ɗan bindiga ɗaya.
Rundunar sojojin ƙasa ta Najeriya ta tabbatar da samun wannan nasara a shafinta na manhajar X wanda aka fi sani da Twitter a ranar Laraba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sojoji sun gwabza da ƴan bindiga
Sojojin sun yi wa 'yan bindigar kwanton bauna a kewayen kauyen Kwaga, inda suka kashe daya yayin da sauran suka gudu ɗauke da raunuka.
An tattaro cewa tawagar ƴan bindigar sun yi kaurin suna wajen yawan kai hare-hare kan bayin Allah a ƙaramar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna.
Sanarwar rundunar sojojin ta ƙara da cewa ɗaukin da gwarazan sojojin suka kai ya zama silar hana ƴan bindigar kai farmaki kan mutane a yankin.
Dakarun sojojin sun kuma kwato bindigu kirar AK-47 guda biyu da magazines, da kuma babura biyu a lokacin arangama da ƴan ta'addan.
Sanarwan ta ƙara da cewa, "Yanzu haka jami'an sojojin sun bazu neman ƴan bindigar da nufin kama su."
Sojoji sun kashe hatsabibin ɗan bindiga
Wannan na zuwa ne kwanaki kalilan bayan sojoji sun yi nasarar kashe ƙasurgumin ɗan bindiga da ya addabi al'umma, Dogo Bagaje a jihar Kaduna.
Lamarin ya faru a karamar hukumar Giwa da ke jihar inda aka tafka mummunan faɗa wanda ya yi sanadin mutuwar Bagaje da wasu miyagun 'yan bindigan.
Mutum 8 sun mutu a harin masallacin Kano
A wani rahoton kun ji cewa wasu ƙarin mutum bakwai daga cikin waɗanda suka samu rauni a harin masallaci a jihar Kano sun riga mu gidan gaskiya.
Hakan ya sa adadin waɗanda suka mutu a harin ya zama mutum takwas yayin da sauran mutane 17 ke kwance a asibitin Murtala Muhammad
Asali: Legit.ng