"Babu Ɗan Takara Ko Jam'iyya da Za Su Gyara Najeriya", Dan Takarar Shugaban Kasa

"Babu Ɗan Takara Ko Jam'iyya da Za Su Gyara Najeriya", Dan Takarar Shugaban Kasa

  • Yayin da ake shirye-shiryen haɗaka na jam'iyyun adawa, daya daga cikin ƴan takarar shugaban kasa ya magantu kan lamarin
  • Pat Utomi wanda ya yi takarar shugaban kasa a zaben baya ya ce a yanzu ƴan siyasa kawai suna yin mulki domin kansu ne ba wai yan kasa ba
  • Ya ce kuma a yanzu babu wani ɗan takara ko wata jam'iyyar siyasa da za ta kawo ci gaban da yan kasar suke tsammani

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Tsohon ;dan takarar shugaban kasa a zaben Najeriya, Pat Utomi ya magantu kan yadda za a inganta kasar nan.

Farfesa Pat Utomi ya ce babu wani dan takara ko jam'iyya a kasar da za su iya kawo ci gaban da ake bukata a Najeriya.

Kara karanta wannan

'Tinubu ya yi watsi da mu bayan zaben 2023', shugabannin mata na APC sun koka

Dan takarar shugaban kasa ya fadi halin da Najeriya ke ciki
Dan takarar shugaban kasa a baya, Pat Utomi ya magantu kan hadakar jam'iyyun adawa. Hoto: @Utomipat.
Asali: Twitter

Utomi ya magantu kan haɗakar jam'iyyun adawa

'Dan takarar ya bayyana haka ne yayin da jam'iyyun adawa ke shirye-shiryen hada kai domin kalubantar APC mai mulki a 2027, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shirin hadakar ya kara karfi bayan ziyarar da ɗan takarar shugaban kasa a LP, Peter Obi ya kai wa Atiku Abubakar, cewar Vanguard.

Utomi ya koka kan halin ƴan siyasa

"Ƴan siyasa ba za su ceto kasar nan ba, haka jam'iyyun siyasa su ma ba za su kawo cigaban da ake bukata ba, dole ƴan kasa su kwace ta daga gare su."
"Ƴan siyasa sun bar yin aiki ga jama'a sai dai domin kansu kawai, shiyasa babu jam'iyyar siyasa da yanzu za ta kawo cigaba a kasar Najeriya."

- Pat Utomi

Utomi ya bayyana yadda tsarin Najeriya ya ke a yanzu inda ya ce zai yi wahala ƴan tsiraru su iya gyara kasar.

Kara karanta wannan

Matsala ga Tinubu yayin da Atiku Abubakar ya gana da Peter Obi, bayanai sun fito

Tinubu ya tallafa a aikin hajji

A wani labarin, kun ji cewa shugaban kasa, Bola Tinubu ya ba da tallafin N90bn domin saukakawa maniyyata yayin aka kara kudin kujerar hajji.

Mataimakin shugaban kasar, Kashim Shettima shi ya bayyana haka a yau Laraba 15 ga watan Mayu a birnin Kebbi da ke jihar Kebbi.

Shettima ya ce Tinubu ya himmatu wurin inganta darajar Naira domin farfaɗo da tattalin arzikin kasar nan kusa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.