Jerin Ma’ikatun Gwamnati Sama da 30 Marasa Biyan Kudin Wuta Duk da Ware N10bn

Jerin Ma’ikatun Gwamnati Sama da 30 Marasa Biyan Kudin Wuta Duk da Ware N10bn

  • Ma'aikatun gwamnati sama da 34 ne ake bi bashin kudin wutar lantarki duk da cewa suna karbar kudin wuta duk shekara
  • Cikin jerin manyan ma'aikatun da ake bi bashi sosai har da fadar shugaban kasa da hedikwatar sojin da 'yan sandan Najeriya
  • A wannan rahoton Legit ta tattaro muku manyan ma'aikatun da ake binsu bashin tare da lissafa kudaden da ake binsu

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja - Wani bincike kan kudin wutar lantarki ya nuna cewa akwai yiwuwar da yawa cikin ma'aikatun gwamnatin tarayya da ke Abuja sun yi sama da fadi da kudaden da aka ware domin biyan kudin wuta.

Kara karanta wannan

"Akwai yiwuwar gwamnatin Tinubu ta kara kasafin 2024 domin gyara albashin ma'aikata," IMF

AEDC ABUJA
Bashin kudin wuta ya yi wa ma'aikatun gwamnati katutu a Abuja. Hoto: Pius Utomi Ekpei
Asali: Facebook

Binciken ya nuna cewa duk da dimbin kudade da gwamnati ta ware tsakanin shekarar 2021 zuwa 2023 kamfanin raba wuta na Abuja (AEDC) ya biyo ma'aikatu da yawa bashi.

Rahoton da jaridar Leadership ta fitar ya nuna cewa sama da ma'aikatu 34 ne ciki har da fadar shugaban kasa kamfanin raba wutar ke bi bashi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wuta: Nawa ake bin ma'aikatun bashi?

Jimillar kudaden da ake bin ma'aikatun ya haura sama da N10b duk da cewa gwamnatin tarayya na ware musu kuɗin wuta duk shekara.

Wannanar badakalar da aka samu ta rashin biyan kudin wuta dai za ta cigaba da zama nauyi a kan gwamnatin tarayya na tsawon lokaci.

Yunkurin yanke wutar fadar shugaban kasa

Saboda yawan bashin ne kamfanin AEDC a farkon wannar shekarar ya yi barazanar yanke wuta ga manyan ma'aikatu ciki har da fadar shugaban kasa.

Kara karanta wannan

"Wannan ai sata ce," NLC ta magantu kan karin kudin wutar lantari a Kogi

A lokacin da kamfanin ya yi barazanar ya sanar da cewa yana bin fadar shugaban kasa da sauran ma'aikatun N47b.

Hedikwatar rundunar sojin Najeriya ita ce ma'aikata da ta fi yawan bashin kudin wuta wanda ana binta bashin N12b.

Ma'aikatun da AEDC ke bi bashin wuta

1. Fadar shugaban kasa: Naira miliyan 923

2. Ma’aikatar birnin tarayya: Naira biliyan 7.5

3. Ma’aikatar kudi: Naira biliyan 5.4

4. Ofishin Gwamnan Jihar Neja: Naira biliyan 3.4

5. Ƙaramar Ma’aikatar Man Fetur: Naira biliyan 2.1

6. Ma’aikatar ilimi: Naira biliyan 1.8

7. Bankin CBN: Naira biliyan 1.5.

8. Hedikwatar rundunar ‘yan sandan Najeriya, Naira biliyan 1.3

9. Ofishin Gwamnan Jihar Kogi: Naira biliyan 1.3

10. Ma’aikatar Lafiya: Naira Biliyan 1.1

Ba a saka ma'ikatun cikin kasafin kudi ne?

Binciken ya nuna cewa dukkan ma'aikatun an ware musu kudade domin biyan kudin wuta cikin shekaru amma ba su biya kamfanin wutar ba.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun kama yan bindiga da matsafi da gashin mutum

Misali an ware wa fadar shugaban kasa N745,793832m a matsayin kudin wuta cikin shekaru uku amma an biyota bashin kudin wuta N923m, rahoton the Cable.

FCDA za ta yi rusau a Abuja

A wani rahoton, kun ji cewa hukumar kula da birnin tarayya Abuja (FCDA) ta sanar da fara ayyukan rusau kan wasu shaguna da aka gina ba bisa ka'ida ba.

Jami'in hukumar, Garba Jibril ya tabbatar da cewa za a rusa shaguna 500 ne domin suna kawo tsaiko kan ayyukan cigaba a babban birnin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng