Sambisa: Sojojin Najeriya Sun Fafata da Boko Haram, an Kashe Babban Aminin Shekau

Sambisa: Sojojin Najeriya Sun Fafata da Boko Haram, an Kashe Babban Aminin Shekau

  • Rundunar sojoji ta Operation Hadin Kai sun bayyana cewa sun kashe wani babban shugaban 'yan Boko Haram, Tahir Baga
  • Legit Hausa ta tattaro cewa an kashe Baga, wanda aminin Shekau ne a lokacin da sojojin suka kai wani samame a dajin Sambisa
  • Miliyoyin mutane ne suka rasa matsugunansu a jihohin Borno, Adamawa da Yobe, jihohi uku da rikicin Boko Haram ya fi shafa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Sambisa, jihar Borno – Sojojin Najeriya sun kashe wani babban shugaban Boko Haram, Tahir Baga.

Sojoji sun kashe babban shugaban Boko Haram.
An kashe Tahir Baga, babban aminin Shekaru, kuma shugaban Boko Haram. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Tahir Baga, babban aminin Abubakar Shekau

An kashe Tahir a ranar Litinin, 13 ga watan Mayu, 2024, a dajin Sambisa, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito a ranar Talata, 14 ga watan Mayu.

Kara karanta wannan

Babu Bahaushe ko 1: Jerin manyan mawaka 10 mafi arziki a Nigeria a 2024

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wata majiya, Zagazola Makama, ta ce:

“Tahir Baga, ya kasance amini ne ga Abubakar Shekau. Yana daga cikin wadanda suka kafa kungiyar Boko Haram a Maiduguri kafin su shige dajin Sambisa.
"A lokacin ya koma tare da irin su Mamman Nur, Khalid Albarnawi, Abubakar Shekau, Kaka Ali, Mustapha Chad, Abu Maryam da Abu Krimima."

Yadda Baga yake yaudarar 'yan Boko Haram

Kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Twitter, Makama ya kara da cewa:

“Tahir Baga, babban Limami ne wanda ake girmamawa a cikin Boko Haram. Ya sha canja ra'ayin mayakan kungiyar da iyalansu daga yunkurin mika wuya ga sojoji ko gwamnati.
Ya kuma ingiza ’yan mata da yawa wadanda ba su kai shekarun balaga ba su kai harin bam bayan ya yi masu hudubar za su shiga aljanna a matsayin ladar kunar bakin wake.”

Kara karanta wannan

'Renewed Hope': Ministan Tinubu ya raba buhunan shinkafa 10,000 a jihar Oyo

Mun sha ruwaito cewa kungiyar Boko Haram ta kashe mutane da dama tare da raba miliyoyi da muhallansu a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.

Miliyoyin mutane ne suka rasa matsugunansu a jihohin Borno, Adamawa da Yobe, jihohi uku da rikicin Boko Haram ya fi shafa.

Dan tsohon shugaban ISWAP ya mika wuya

A wani labarin, mun ruwaito maku cewa, Mahmud Mamman Nur Albarnawy, dan wanda ya kafa kungiyar ta'addanci ta ISWAP, ya mika wuya ga rundunar tsaro ta NSCDC.

An ce Mahmud Mamman Nur mamba ne a kungiyar Boko Haram da ke ta'addanci a garuruwan jihar Borno da wasu sassa na jihohin Arewa maso Gabas kafin ya mika wuya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.