'Yan Bindiga Sun Tarwatsa Ƙauyuka 50, Sun Sace Mutane Sama da 500 a Arewa
- Ƴan bindiga sun tarwatsa mutane a kauyuka 50 a ƙaramar hukumar Zurmi da ke jihar Zamfara a Arewa maso Yamma
- Mamba mai wakiltar Zurmi da Shinkafi a majalisar wakilai ta ƙasa, Bello Hassan ya ce ƴan bindiga na kai hari kan jama'a ba dare ba rana
- Ya bukaci hukumomin tsaro su kara tura jami'ai zuwa yankin kuma su canza salon yaki da ƴan bindigar domin samun nasara
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Zamfara - Hare-haren ƴan bindiga ya tilastawa mazauna kauyuka 50 neman mafaka a wurare daban-daban a ƙaramar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara.
An tattaro cewa galibin mazauna kauyukan sun bar gidajensu domin tsira daga ta'addancin ƴan bindiga a jihar da ke shiyyar Arewa maso Yamma.
Ɗan majalisa mai wakiltar Zurmi da Shinkafi a majalisar wakilan tarayya, Bello Hassan ne ya bayyana haka a wata hira da BBC Hausa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Halin da mutanen Zurmi ke ciki
A makon jiya, Premium Times ta ruwaito yadda ‘yan ta’adda suka mamaye garin Zurmi wanda shi ne gari na biyu mafi yawan jama’a a jihar Zamfara.
Yayin harin ƴan bindigar sun kashe mutum uku a fadar sarkin Zurmi tare da yin awon gaba da wasu mazauna garin da dama.
Ƴan bindiga sun sace mutane 500
Ɗan majlalisar ya bayyana cewa ana tsammanin ƴan bindiga sun yi garkuwa da mutane sama da 500 a waɗannan kauyuka cikin makonni ƙalilin da suka gabata.
Ya ce hare-hare na rashin imani da tausayi ya tilastawa mutanen kauyukan hakura da rayuwa a gidajensu, inda suka yi gudun hijira zuwa wasu yankunan.
Hon. Hassan ya ƙara da cewa ragowar waɗanda suka zauna kuma suna fuskantar wulaƙanci da cin zarafin yan bindiga dare da rana.
Ya kamata jami'an tsaro su sauya salo
Ya ce:
“A kauyen Kanwa, ‘yan bindigar sun kashe mutane uku tare da sace wasu sama da 30 ranar Asabar. A Gidan Shaho kuma sun kashe ‘yan sanda biyu tare da raunata mutane da dama.
"Yanzu muna kokarin gano adadin mutanen da suka bata bayan harin (na baya-bayan nan). Akwai bukatar a sake nazari kan wasu hanyoyin da jami’an tsaro ke bi wajen yakar ‘yan ta’adda a Zamfara."
Hassan ya bukaci hukumomin tsaro da su kara tura jami'ai zuwa yankin tare da sauya salon yaki da 'yan bindiga.
Yan bindiga sun kai hari a Benue
A wani rahoton kuma akalla mutane 11 ne 'yan bindiga suka kashe a wani hari da suka kai kauyen Ole’Adag’aklo da ke gundumar Usha a jihar Benue.
Shugaban karamar hukumar Agatu, Yakubu Ochepo, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce 'yan bindigar sun tafi da wasu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng