"Akwai Yiwuwar Gwamnatin Tinubu ta Kara Kasafin 2024 Domin Gyara Albashin Ma'aikata," IMF

"Akwai Yiwuwar Gwamnatin Tinubu ta Kara Kasafin 2024 Domin Gyara Albashin Ma'aikata," IMF

  • Bankin bayar da lamuni na duniya (IMF) ta shawarci gwamnatin Najeriya ta samar da wata kwarya-kwaryar kasafi matukar za a biya sabon mafi karancin albashi
  • Sabon kasafin zai dama dole idan tattaunawa ta fada tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyoyin kwadago na neman kara mafi karancin albashi ga ma’aikatan kasar nan
  • Haka kuma IMF din ta ce dole sai gwamnati ta kara ranto kudi daga bankuna da sauran masu bayar da bashi idan ta na son daukar dawainiyar da ke gabanta

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja-Alamu na nuna cewa akwai yiwuwar gwamnatin tarayya ta samar da kwarya-kwaryan kasafi matukar za ta biya karin albashin ma’aikata da kungiyoyin kwadago ke ta fafutukar a yi.

Kara karanta wannan

"Wannan ai sata ce," NLC ta magantu kan karin kudin wutar lantari a Kogi

Sabon kasafin na kwarya kwarya zai zama dole ne ganin cewa kudin da gwamnati ta ware na biyan ma’aikata a 2024 ba zai wadata ba.

Tinubu imf
IMF ta shawarci gwamnatin Bola Tinubu ya samar da kwarya-kwaryar kasafi Hoto: Bola Ahmed Tinubu, olivier douliery
Asali: Facebook

Bankin bayar da lamuni na duniya (IMF) ne tun da fari ya ba Najeriya shawarar a cikin rahoton da ya fitar kan kasar, kamar yadda Punch News ya wallafa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton ya ce:

“Akwai yiwuwar hukumomi su bakaci kwarya-kwaryar kasafin domin samun damar iya biyan sabon mafi marancin albashi da ake sa ran za a cimma da za su iya fin karfin kasafin 2024.”

IMF ta ba Najeriya shawara kan rance

Wani rahoton da bankin bayar da lamuni na duniya (IMF) ya shawarci gwamnatin Najeriya ta duba yiwuwar cin bashin kudi daga wasu wuraren domin iya daukar nauyin biyan bukatun gabanta.

Rahoton bankin ya bayyana cewa bankuna da sauran masu bayar da rance za su taimakawa gwamnatin da rance matukar akwai kudin ruwa mai gwabi-gwabi, kamar yadda Nairaland ta wallafa.

Kara karanta wannan

Wahalar Rayuwa: Ka da a Karaya da Mulkin Bola Tinubu, Jigon APC Ya Lallabi Mutane

Haka kuma sai an samu karin abubuwan da ake hadawa A Najeriya da kaso 1.3% a kan yadda aka samar a shekarar 2023, kuma IMF din ta shawarci kasar nan ta rage rancen kudi daga babban bankin kasa CBN.

IMF na zuga gwamnatin Najeriya

A baya mun kawo muku labarin cewa asusun ba da lamuni na duniya (IMF), na tunzura gwamnatin Najeriya ta kara farashin kudin wuta yayinda ake fama da talauci.

Bankin ya yi sabon kira ga gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ya kammala cire tallafin man fetur da wutar lantarki ga ‘yan kasar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel