'Yan Bindiga: Aliero Sun Tafka Barna, Sun Hallaka Sojoji 5, Jikkata Wasu 11 a Katsina
- Wasu 'yan bindiga karkashin jagorancin Ado Aliero sun farmaki dakarun sojoji inda suka tafka musu barna a jihar Katsina
- Maharan sun hallaka sojoji akalla guda biyar da kuma jikkata 11 a gumurzun da suka yi a karamar hukumar Faskari a jihar
- Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi 12 ga watan Mayu a sansanin dakarun da ke kauyen Yar Malamai da ke jihar ta Katsina
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Katsina - Mummunan fada ya kaure tsakanin dakarun sojoji da kuma 'yan bindiga a jihar Katsina.
Lamarin ya yi sanadin mutuwar sojoji biyar da raunata 11 yayin harin a sansanin sojoji da ke karamar hukumar Faskari a jihar.
Yaushe ƴan bindiga suka hallaka sojoji?
Harin ya faru ne da misalin karfe 2:00 na rana a ranar Lahadi 12 fa watan Mayu inda fararen hula suka rasa rayukansu da wani dan banga, cewar Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Premium Times ta tattaro cewa hatsabibin ɗan bindiga, Ado Aleiro shi ya jagoranci maharan kusan 200 zuwa sansanin a kauyen Yar Malamai.
"Yan ta'adda sun kai farmaki sansanin sojoji a jihar Katsina wanda ya yi sanadin mutuwar sojoji da dama."
- Majiyar tsaro
Ƴan bindiga sun kashe 'dan banga
Daga cikin wadanda suka rasa ransu akwai ɗan banga mai suna Tukur Ali wanda bai wuce shekaru 30 ba a duniya.
Farmakin wanda ya shafe tsawon awanni biyu ya tilasta dakarun sojojin ja da baya domin tsira zuwa wani wuri amintance.
Har ila yau, ƴan ta'addan sun tafka asara suma a bangarensu yayin da suka kawo farmakin.
Bayan nan ne miyagun suka shiga cikin kauyen Yar Malamai, aka kona gidaje tare da tafka mummunan barna.
Sojoji sun hallaka hatsabibin ɗan bindiga
A wani labarin, kun ji cewa dakarun sojoji sun yi ajalin wasu kasurguman 'yan bindiga guda hudu a jihar Kaduna yayin wani farmaki.
Sojojin sun hallaka maharan ne gida hudu ciki har da shugaban ƴan ta'adda mai suna Dogo Bangaje yayin wani artabu.
Dakarun sun yi nasarar hallaka miyagun ne bayan samun bayanai sirri a wasu ƙauyuka biyu da ke karamar hukumar Giwa a jihar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng