Mutanen Arewa Sun Taso Ministan Tinubu a Gaba Sai Ya Yi Murabus Daga Kujerarsa
- Yayin da matsalar wutar lantarki a yankin Arewa maso Gabas ke kara ƙamari, mutanen yankin sun kosa kan halin da suke ciki
- Jama'ar yankin sun bukaci Ministan makamashi, Adebayo Adelabu da ya yi murabus daga kujerarsa kan halin da ake ciki
- Legit Hausa ta ji ta bakin wasu mazauna yankin da kuma jami'ar hukumar JED kan wannan lamari na rashin wutar lantarki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Ministan makamashi a Najeriya, Mista Adebayo Adelabu ya shiga matsala yayin da ake kiran ya yi murabus daga kujerarsa.
Mutanen yankin Arewa musamman ta bangaren Arewa maso Gabas sun taso Ministan a gaba kan lalacewar wutar lantarki a yankin tsawon makwanni.
Arewa ta shiga duhu na rashin wuta
Wani kwararren lauya daga jihar Taraba, Bilyaminu Maihanchi shi ya yi wannan kira ga Ministan yayin da wutar yankin ke kara tabarbarewa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Cikin budaddiyar wasikar da Maihanchi ya fitar a jiya Litinin 13 ga watan Mayu, ya bukaci Ministan ya yi gaggawar yin murabus, cewar The Guardian.
Maihanchi ya bayyana irin asara da kuma illar rashin wutar a yankin da ya durkusar da tattalin arzikin yankin.
Lauyan ya ce rashin wutar ya gurgunta tattalin arziki da bangaren lafiya da ilimi da sauran harkokin rayuwa, cewar Daily Post.
"Mutanen yankin Arewa maso Gabas suna cikin kunci na rashin wuta da ya gurgunta tattalin arziki da lafiya da ilimi da kuma sauran harkokin rayuwa."
- Bilyaminu Maihanchi
Lauya ya bukaci bincike kan wutar lantarki
Bilyaminu ya bukaci bincike da tabbatar da sauyin shugabanci a ma'aikatar wutar lantarki da kuma murabus na Ministan.
Ya ce hakan zai samar da shugabanci nagari domin tabbatar da kawo karshen wannan matsalar wuta a yankin Arewa maso Gabas.
Wannan na zuwa ne bayan daukewar wuta a yankin kusan wata daya kenan bayan miyagu sun tarwatsa husumiyoyin wutar.
Legit Hausa ta tattauna da mazauna Gombe
Legit Hausa ta ji ta bakin wasu mazauna yankin da kuma jami'ar hukumar JED kan lamarin.
Khadija Abdullahi da ke aiki da kamfanin ta ce an samu matsala ne bayan mahara sun farmaki husumiyoyin wutar lantarki.
Ta ce duk da ana sa ran gyara wutar zuwa 27 ga wannan wata, ta bukaci mutane su kara hakuri kan matsalar rashin wutar.
Abubakar Yunusa, wani mazaunin birnin Gombe ya ce a gaskiya rashin wutar ya kassara tattalin arzikin mutane da dama.
"Babu abin da zamu ce kan matsalar wutar, amma gaskiya muna cikin wani hali."
"Duk da an ce za a iya gyara ta zuwa karshen wata amma muna kira da kada a ci gaba da bamu wuta kamar yadda aka yi lokacin azumi."
- Abubakar Yunusa
NLC ta fusata kan karin kudin wuta
Kun ji cewa shugaban kungiyar kwadago ta NLC reshen jihar Kogi, Kwamred Gabriel Amari ya ce karin kudin wutar lantarki sata ne da tsakar rana.
Shugaban kungiyar ma'aikatan ya ce dole ne gwamnati ta yi gaggawar dawo da kudin wutar yadda ya ke a baya domin saukakawa al'umma.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng