Sojoji sun Kwamushe Masu Zanga Zanga a Jami’a Saboda Karin Kudin Makaranta
- Rahotanni sun nuna cewa rikici ya barke a jami'ar Ibadan a lokacin da ke zanga-zangar adawa da karin kudin makaranta
- Shugabannin dalibai sun tabbatar da cewa sojojin da ke tsaron makarancikin masu zanga-zangar
- Wani dalibi da ya bukaci a boye sunansa saboda fargabar tsaro ya bayyanawa manema labarai yadda lamarin ya faru
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Oyo - Rikici ya barke a jami'ar Ibadan da ke jihar Oyo sakamakon zanga-zangar adawa da karin kudin makaranta.
Rahotanni sun nuna cewa rundunar sojojin Najeriya ta kama cikin masu zanga-zangar adawa da karin kuɗin.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa mutanen da sojojin sun kama sun hada da Aduwo Ayedole, Made Gbadegesin, Olorunfemi Adeyeye da Nice Linus.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sojojin sun kama masu adawa da karin kudin ne tare da cusa su cikin mota a yayin zanga-zangar, rahoton Sahara Reporters.
Yadda sojoji suka kama masu zanga-zangar
Magatakardan kungiyar African Action Congress, Olorunfemi Adeyeye ya wallafa faifayin bidiyo kan yadda aka kama masu zanga-zangar.
Adeyeye ya tabbatar da cewa jami'an tsaro ne da suke aiki a jami'ar suka kama su tare da jan su a kasa.
Yadda zanga-zangar ta fara a jami'a
Wani dalibi da ya nemi a boye sunansa ya bayyana cewa lamarin ya faru ne daidai lokacin da ake rantsar da sababbin shugabannin dalibai.
A cewarsa, ana tsaka da rantsar da shugabannin ne sai dalibai masu zanga-zangar suka bayyana kwatsam suna rike da alluna.
Zanga-zanga: Hukumomi ba suce komai ba
Har zuwa lokacin wallafa labarin Legit ba ta samu jin ta bakin kakakin rundunar sojan Najeriya, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ba.
Haka zalika jin ta bakin shugaban harkokin dalibai na jami'ar, Farfesa Adekeye Abiona ya ci tura.
Kungiyar dalibai ta yi fatali da karin kudin
Tun a watan Afrilu ne dai kungiyar daliban Najeriya ta kasa ta yi Allah wadai da karin kudin makaranta da jami'ar ta yi.
Rahotanni sun nuna cewa jami'ar ta kara kudin makarantar ne har zuwa N230,000 zuwa N412,000 a zangon karatun 2023/2024.
Daliban jami'ar jos sun yi zanga zanga
A wani rahoton, kun ji cewa yayin da ake gasar karin kudin makaranta a jami’o’i, daliban Jami’ar Jos sun ce ba su amince da karin kudin da aka musu ba.
Rahotanni sun tabbatar da cewa daliban jami’ar ta Jos sun fito zanga-zanga don nuna damuwarsu kan lamarin da kuma bukatar a janye maganar karin kudin.
Muhammad Malumfashi, babban editan sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng