Karin Kudin Wutar Lantarki: Kungiyar Kwadago Ta Rufe Ginin Kamfanin DisCos a Jos

Karin Kudin Wutar Lantarki: Kungiyar Kwadago Ta Rufe Ginin Kamfanin DisCos a Jos

  • Kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC) ta rufe hedikwatar kamfanin rarraba wutar lantarki na Jos (JEDC) da ke jihar Plateau
  • An ruwaito cewa mambobin kungiyar sun fara rufe ofisoshin DisCos saboda gaza janye karin kudin wutar lantarki da suka yi
  • Mazauna Hayin Rigasa da unguwar Mu'azu, da muka tattauna da su, sun bayyana halin da wutar ta ke a wajen su

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jos, jihar Plateau - Kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC) ta rufe hedikwatar kamfanin rarraba wutar lantarki na Jos (JEDC) da ke jihar Plateau saboda karin kudin wutar da aka yi.

Kungiyar kwadago ta rufe ofishin JEDC da ke jihar Plateau
Kungiyar NLC ta rufe kamfanin JEDC saboda karin kudin wutar lantarki. Hoto: @NLCHeadquarters
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, kungiyar kwadagon ta tare babbar kofar shiga kamfanin, inda ma’aikatan DisCo din suka yi cirko-cirko a waje.

Kara karanta wannan

Rikicin Rivers: EFCC ta na neman gwamnan PDP ruwa a jallo? Gaskiya ta fito

An ga jami’an tsaro da suka hada da ‘yan sanda, DSS da jami’an tsaro na farin kaya (NSCDC) a kofar shiga kamfanin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NLC ta nemi janye karin kudin wuta

Mun ruwaito maku yadda NLC da TUC suka sanar da cewa za su rufe ofisoshin hukumar NERC da kamfanonin DisCo a fadin kasar idan suka ki janye karin kudin wuta da aka yi.

Sannan mun ruwaito hukumar NERC ta kara kudin wutar lantarki daga N65/kwh zuwa N225/Kwh ga abokan hulda da ke karkashin rukunin 'Band A'.

Daga baya ne gwamnatin tarayya ta amince da matakin rage kadan daga kudin, wanda 'yan kwadago suka yi watsi da shi.

"Wata 2 ba su karbi kudi ba" - Mutane

A yayin da kungiyoyin kwadago ke ci gaba da mamaye gine-ginen kamfanonin DisCo, mun tattauna da mazauna Rigasa, jihar Kaduna game da kudin wutar lantarki da samuwarta.

Kara karanta wannan

"Wannan ai sata ce," NLC ta magantu kan karin kudin wutar lantari a Kogi

Al'amin mai shago ya ce watanni biyu kenan ba a zo karbar kudin wuta a unguwar da ya ke ta Makarfi ba, sai dai su kawo 'bill' amma ba su tambayar kudin wutar.

Mai shagon ya kuma jaddada cewa ana samun wutar lantarki a kai a kai a inda ya ke zama wanda hakan alamar samun ci gaba ne a kasuwancinsa.

Da muka tuntubi Yusuf Muhammad a unguwar Mu'azu, sha tale-talen Nmandi Azikwe a Kaduna, ya ce tabbas an yi karin kudin wuta, amma su bai shafe su ba.

Yusuf Muhammad ya ce har yanzu 'bill' din N5,800 da ake kai wa gidansu shi ne suke karba ba tare da kari ba, kuma wutar lantarkin na samuwa jefi jefi.

Ya ce akwai bukatar kamfanonin rarraba wutar lantarki su samar da na'u'rorin 'mita' ga gidaje wanda zai kawo tsarin "iya kudin ka iya shagalin ka."

Majalisar wakilai ta ba NERC umarni

Kara karanta wannan

Wutar lantarki: 'Yan kwadago sun fusata, sun rufe ofishin hukumar NERC a Abuja

A wani labarin, mun ruwaito cewa majalisar wakilai ta ba hukumar kula da wutar lantarki ta Najeriya (NERC) umarnin janye karin kudin wutar da ta yi wa 'yan rukunin 'Band A'.

Majalisar ta dauki matakin ne bayan amincewa da wani kudiri mai muhimmanci ga jama'a da Hon. Nkemkanma Kama ya gabatar kan illolin karin kudin a dai-dai wannan lokaci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel