Ranar Ma'aikatan Jinya: Yadda Maza ke Ganin Wariyar Jinsi da Matsaloli a Asibiti

Ranar Ma'aikatan Jinya: Yadda Maza ke Ganin Wariyar Jinsi da Matsaloli a Asibiti

  • Yayin da ake bikin ranar ma'aikatan jinya ta duniya, rahotanni sun nuna cewa ana samun karuwar maza suna shiga aikin a Najeriya
  • A kasar Amurka an wallafa rahoto cewa a shekarar 2023, akalla kaso 12% na ma'aikatan jinyar da suka samu lasisin aiki maza ne
  • Amma ma'aikatan jinyar a Kano sun bayyana damuwa kan yadda suke fusknatar wariyar jinsi daga abokan aikinsu da sauran marasa lafiya a asibitoci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kano-Yayin da ake bikin ranar ma'aikatan jinya ta duniya a ranar 12 ga watan Mayu, rahotanni sun nuna cewa ana samun karuwar maza suna shiga aikin.

Kara karanta wannan

Kakakin majalisar jihar Niger zai aurar da marayu 100

A kasar Amurka, mujallar nurse journal ta wallafa cewa akalla kaso 12% na ma'aikatan jinyar da suka samu lasisin aiki maza ne.

Nurse Buhari Abubakar Isa
Ma'aikatan jinya maza na karuwa a asibitoci Hoto: Nr Buhari Abubakar Isa
Asali: UGC

Maza da ke aikin jinya a asibitoci

Duk da a Najeriya ba a fitar da alkaluman maza da ke shiga aikin jinya ba, ana samun karuwarsu ainun.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daya daga jami'an jinya maza a Kano, Nr Buhari Abubakar Isah ya shaidawa Legit Hausa yadda maza ke kara tururuwar shiga aikin jinya.

Ya ce a yanzu, alkaluma sun nuna cewa a cikin ma'aikatan jinya 10, daya ne kawai namiji, wanda yake ganin akwai bukatar maza su shiga aikin jinyar marasa lafiya a asibitoci.

"Maza na fuskantar wariya", Nr Isah

Wani ma'aikacin jinya a Kano, Nr Buhari Abubakar Isah ya bayyana cewa maza na fuskantar wariyar jinsi.

Kara karanta wannan

Manyan Janar 29 sun yi ritaya daga gidan soja ana tsaka da rashin tsaro

Ya ce mafi akasarin wadanda ke aikin jinya mata ne, amma yanzu maza ma suna cikin aikin sosai.

A kalamansa:

"Bana jin dadin yadda wasu abokan aiki 'sister', duk da ina amsawa amma bana jin dadi."

Ya ce bambancin jinsin da suke samu yana basu matsala da marasa lafiya da 'yan uwansu, domin a cewarsa:

"Ba su za su iya kiran ka da 'nas' ba ko ma'aikacin jinya. A gurin sai dai ka ji masu ilimin ma sun kira ka likita, sun hada ka da likita."

Ya ce:

"A wasu wuraren kuma sai dai ka ji ana kiran ka sidda sidda, ma'ana sister ke nan."

Ya kara da cewa marasa mata ko mazajensu ko iyayensu ba sa jin dadin cewa namiji ne ma'aikacin jinyar da zai kula da su.

Babu isassun wurin sauya kaya

A cewar ma'aikacin jinyar, daya daga kalubalen da suke fuskanta a matsayinsu na maza shi ne rashin wurin sauya kaya.

Kara karanta wannan

InnalilLahi: 'Yan bindiga sun bindige ma'aikacin FIRS a tsakiyar birnin Abuja

Ya ce kusan dukkanin asibitocin dake Kano na da wurin sauya kaya daya ne kawai, su ma na mata ne.

Ma'aikacin ya ce wasu lokutan idan sun taho da kayansu daga gida, ba sa sakewa wajen sauyawa domin wasu lokutan sai sun jira matan sun fito daga dakin sauya kayan.

Nr Buhari ya kara da cewa ko wurin hutawa na ma'aikatan jinyar daya ne, kuma mata sun mamaye shi.

Za a biya daliban jinya N30,000

A baya kun samu labarin yadda gwamnatin jihar Borno ta yi alkawarin biyan dukkan daliban jinyar dake jihar N30,000 duk wata.

Gwamna Babagana Umara Zulum ne ya yi alkawarin, inda ya ce za kuma a rika bayar da wasu tallafin karatun ga daliban.

Muhammad Malumfashi, babban editan sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.