Coronavirus: Hotunan cibiyar killacewa da gidauniyar Dangote ta gina a Kano

Coronavirus: Hotunan cibiyar killacewa da gidauniyar Dangote ta gina a Kano

Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya kai ziyara cibiyar killace masu dauke da cutar covid-19 da gidauniyar Dangote tare da hadin gwuiwar gwamnatin jihar Kano suka samar.

Cibiyar, mai jimillar gadon kwantar da marasa lafiya 509, tana da bandakuna, dakin gwaji, dakin shan magani, motar daukan marasa lafiiya, dakin ganawar ma'aikata da masana da sauransu.

Tun a ranar 29 ga watan Maris Legit.ng ta wallafa rahoton cewa hamshakin attajirin dan kasuwa, Alhaji Aliko Dangote, zai samar da wata cibiyar killace wa mai gado 600 domin duba wadanda suka kamu da kwayar cutar coronvirus a jihar Kano.

Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ne ya sanar da hakan yayin kaddamar da kwamitin neman kudin taimakawa masu karamin karfi a jihar.

Hakan na kunshe ne a cikin wani gajeren sako da Bashir Ahmad, mai taimakawa shugaban kasa a bangaren sabbin kafafen sadarwa, ya fitar a shafinsa na dandalin sada zumunta a ranar Lahadi, 28 ga watan Maris.

A baya an ji tsoron cewa mai gidauniyar Dangote kuma hamshakin attajirin dan kasuwa, Alahji Ali Dangote, zai iya kamuwa da kwayar cutar coronavirus bayan ya yi mu'amala da Abba Kyari, shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa da aka tabbatar da cewa yana dauke da kwayar cutar.

DUBA WANNAN: Gwamnatin tarayya ta rabawa talakawan Kano biliyan N1.6

A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na tuwita, Dangote ya bayyana cewa ya yi gwajin kwayar cutar covid-19 ne a matsayinsa na dan kasashe da dama sannan shugaba a kasuwanci.

Ya ce yana jagorantar shugabannin a bangaren kasuwanci domin taimakon gwamnati a kokarinta na dakile yaduwar cutar.

Coronavirus: Hotunan cibiyar killacewa da gidauniyar Dangote ta gina a Kano

Cibiyar killacewa da gidauniyar Dangote ta gina a Kano
Source: Twitter

Cibiyar killacewa da gidauniyar Dangote ta samar a Kano
Source: Twitter

Coronavirus: Hotunan cibiyar killacewa da gidauniyar Dangote ta gina a Kano

Cibiyar killacewa da gidauniyar Dangote ta gina a Kano
Source: Twitter

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel