Abubuwa 5 da Tinubu Ya Kamata Yayi Domin Kai Najeriya Tudun Mun Tsira, in Ji Primate Ayodele

Abubuwa 5 da Tinubu Ya Kamata Yayi Domin Kai Najeriya Tudun Mun Tsira, in Ji Primate Ayodele

  • Babban malamin addinin Kirista, Primate Babatunde Ayodele ya zayyana abubuwa biyar da Tinubu ya kamata ya yi domin inganta Najeria
  • Shugaban cocin Inri Evangelical ya ce dole ne Shugaba Bola Tinubu ya fi mayar da hankali kan inganta tattalin arziki da tsaro a kasar
  • A wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafinsa na X, Primate Ayodele ya ce ubangiji ne ya sanar da shi hakan kuma dole ne Tinbu ya duba su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Ejigbo, jihar Legas – Primate Babatunde Elijah Ayodele, shugaban cocin Inri Evangelical, Legas, ya ce dole ne Shugaba Bola Tinubu ya inganta tattalin arziki da tsaro.

Kara karanta wannan

Atiku Bagudu ya fadi abin da 'yan siyasa ke son yi shekaru da dama da Tinubu ya aiwatar

Mun ruwaito maku cewa Tinubu ya hau mulki ne a shekarar 2023 da nufin cimma kudurinsa mai taken ‘Renewed Hope’.

Primate Ayodele yayi magana akan yadda shugaba Tinubu zai inganta tattalin arzikin Najeriya.
Primate Ayodele ya zayyana abubuwa 5 da Tinubu zai yi domin inganta tattalin arzikin Najeriya. Hoto: Primate Babatunde Elijah Ayodele, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Gwamnati ta yi alkawarin mayar da hankali kan samar da ayyukan yi, samar da jari ga kanana da manyan ‘yan kasuwa, hada kai, bin doka da oda, da yaki da yunwa, fatara da cin hanci da rashawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Primate Ayodele ya ba Tinubu shawara

Da yake magana a cikin wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafinsa na X, Primate Ayodele ya ce Tinubu na bukatar magance damuwar ma’aikatan Najeriya.

Malamin ya kuma bukaci shugaban kasar da ya cika alkawarin da ya yi wa ‘yan Najeriya na cewa gwamnatinsa za ta sake fasalin kasar.

Ayodele ya ce:

"Idan har shugaba Tinubu bai yi aiki kan wadannan muhimman abubuwa guda biyar ba, to hakan zai haifar da baraka mai girma a gwamnatinsa.

Kara karanta wannan

Tinubu ya tausaya, ya dakakar da tsarin biyan harajin 0.5% da CBN ya kawo

"Fannin farko da gwamnatin Tinubu ya kamata ta yi aiki a kai shi ne tsaro. Na biyu, tattalin arziki; na uku, makamashi; na hudu, jin dadin ma'aikata, sannan na biyar, batun sake fasali.
“Idan ba a yi aiki kan wadannan abubuwan biyar ba, to gwamnati za ta yi ta tada zaune tsaye ne, za ta rika yin tangal-tangal babu makoma. Abin da Ubangiji ya ce ke nan.

Bangarorin da Tinubu ya kamata ya duba

1. Tsaro

2. Tattalin arziki

3. Makamashi

4. Jin dadin ma'aikata

5. Sake fasalin kasa

Abinci zai wadata a Najeriya - Tinubu

A wani labarin, mun ruwaito maku cewa Shugaba Bola Tinubu ya yi alkawarin wadatar da 'yan Najeriya da abinci kafin wa'adin mulkinsa ya kare.

Bola Tinubu ya bayyana hakan ne a yayin da yake kaddamar da fara aikin titin Bida zuwa Minna mai nisan kilomita 84 a jihar Neja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel