Yayin da Ake Wahalar Man Fetur, Gwamna Zai Rufe Gidajen Mai da Ke Kara Farashi

Yayin da Ake Wahalar Man Fetur, Gwamna Zai Rufe Gidajen Mai da Ke Kara Farashi

  • Gwamnatin jihar Anambra ta sha alwashin kawo karshen almundahana da ake yi a gidajen mai da dama a jihar
  • Kwamishinan albarkatun man fetur a jihar, Anthony Ifeanya shi ya tabbatar da haka a karshen mako a birnin Awka
  • Ifeanya ya ce za su dauki mummunan mataki kan masu kara farashin man da kuma sauya yanayin lita a fadin jihar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Anambra - Gwamnatin jihar Anambra ta shirya daukar mataki kan wahalar mai a faɗin jihar.

Gwamnatin za ta dauki tsattsauran matakai kan kara farashi da sauya yanayin lita da kuma cakuda man da wasu abubuwa.

Gwamna zai dauki mataki kan masu gidajen mai
Gwamna Charles Soludo zai rufe gidajen mai da ke kara farashi a jihar Anambra. Hoto: Charles Soludo.
Asali: Facebook

Gwamna zai dauki mataki kan masu mai

Kara karanta wannan

Matakai 5 da Gwamnatin Tinubu ta dauka da suka jefa ‘yan Najeriya a wahalar rayuwa

Kwamishinan albarkatun man fetur, Anthony Ifeanya shi ya tabbatar da haka a karshen mako a Awka da ke Anambra, cewar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ifeanya ya ce za su fara saka ido kan dukkan ayyukan masu gidajen mai din domin tabbatar da ingancinsu.

Kwamishinan ya gargadi aikata inda ya ce su guji irin haka ko kuma su fuskanci fushin hukuma, Punch ta tattaro.

Zargin da ake kan masu gidajen mai

Wannan na zuwa ne bayan zargin wasu na gudanar da cuwa-cuwa kan saye da siyarwa a gidajen mai wanda aka kai korafi a ma'aikatar albarkatun man fetur da ke jihar.

An gano wasu masu gidajen mai a jihar da suke siyar da litar mai N850 zuwa N970 yayin da wasu suke sauya yanayin lita.

Har ila yau, wasu masu gidajen mai din ana zarginsu da cakuda mai da wasu abubuwa domin ya kara yawa saboda su samu riba sosai.

Kara karanta wannan

"Daukar fetur a jarka zai iya babbake fasinjoji," FRSC ta gargadi masu abubuwan hawa

An bindige matashi a layin gidan mai

A wani labarin, kun ji cewa wani matashi ya rasa ransa yayin turmutsun bin layin gidan mai a jihar Legas.

Matashin Toheeb Eniasa ya rasa ransa ne bayan wasu jami'an tsaro sun bindige shi a cikin gidan man NNPCL da ke yankin Ikoyi a jihar.

Rundunar 'yan sanda a jihar ta tabbatar da faruwar lamarin ta bakin kakakinta, Benjamin Hundeyin inda ya ce an gano mai laifin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.