Mazauna Port Harcourt Sun Damu da Rikicin Wike da Fubara, Sun Mika Bukata Ga Alkalai

Mazauna Port Harcourt Sun Damu da Rikicin Wike da Fubara, Sun Mika Bukata Ga Alkalai

  • A yayin da rikicin siyasa a Rivers ya ki ci ya ki cinyewa, mazauna Port Harcourt, babban birnin jihar, sun fara nuna damuwa a kai
  • Wani lauya, Aghogho Okpako ya yi kira da a gaggauta yanke hukunci kan shari’o’in da ke da alaka da rikicin siyasa a jihar
  • A cewar Okpako, alkalai ne yanzu ke da wuka da nama na dakile ci gaba da rikicin tun da dai an gaza warware matsalolin a siyasance

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Rivers - Wasu mazauna garin Port Harcourt na kira ga bangaren shari’a da su gaggauta yanke hukunci kan shari’o’in da ke da alaka da rikicin siyasa a jihar Rivers.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai farmaki a jami'a, sun yi garkuwa da dalibai a jihar Kogi

An mayar da hankali ne musamman kan shari'ar sahihancin ‘yan majalisar dokokin jihar 25 da suka sauya sheka zuwa jam’iyyar APC daga PDP.

Mazauna Port Harcourt sun fara damuwa kan rikicin siyasar jihar Rivers
Mazauna Port Harcourt sun nemi alkalai su gaggauta kawo karshen rikicin siyasar jihar Rivers. Hoto: @SimFubaraKSC
Asali: Twitter

A cewar wasu mazauna garin da suka zanta da gidan Talabijin na Channels a ranar Asabar, yanke hukunci a kan lokaci zai taimaka wajen kawo kwanciyar hankali a cikin tirka-tirkar siyasar jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rikice-rikicen siyasa da suka mamaye Rivers

Rikicin da ke ci gaba da faruwa, ya samo asali ne daga abubuwan da suka faru a jihar ciki har da yunkurin tsige Gwamna Siminialayi Fubara watanni bakwai da suka gabata.

Haka zalika, akwai rigingimun bangaranci a majalisar dokokin jihar Ribas, wanda ya kara haifar da matsaloli da dama da ba a warware ba har yanzu.

A takaice, jihar na fama da matsalar cancantar ‘yan majalisar da suka sauya sheka, da cece-kuce kan ayyukan majalisar, da kuma sake yunkurin da aka yi na tsige gwamnan jihar.

Kara karanta wannan

"An yi watsi da su": Jigon APC ya magantu kan halin da El-Rufai da Yahaya Bello ke ciki

Duk da kokarin shiga tsakani, zaben sabon kakakin da 'yan majalisa masu goyon bayan Fubara suka yi da kuma hukuncin shari'a na baya-bayan nan, sun nuna cewa har yanzu akwai rashin zaman lafiya a jihar.

Mazauna Rivers sun ba da shawarar mafita

Wadannan abubuwa da ke faruwa sun zama abin damuwa ga mazauna Fatakwal. Wani lauya, Aghogho Okpako ya yi kira da a gaggauta kawo karshen shari’o’in da ke da alaka da rikicin siyasa a jihar

“Ina ganin cewa rikicin da ke faruwa ba shi da wani amfani. Sun yi ƙoƙarin warware rikicin a siyasance amma hakan ya ci tura.
"Don haka, a yayin da ’yan siyasa ke yin nasu kokarin, ina kira ga alkalai da su yi gaggawar magance wannan lamari ta hanyar yanke hukunci kan shari'o'in siyasar da ke gabansu.”

- A cewar Aghogho Okpako.

An mamaye ginin majalisar Rivers

A wani labarin, mun ruwaito maku cewa akalla 'yan sanda dauke da makamai sun mamaye ginin majalisar jihar Rivers musamman bangaren gidajen 'yan majalisar.

Wannan na zuwa ne yayin da 'yan majalisar da ke goyon bayan Nyesom Wike da jiga-jigan APC suka zargi Gwamna Siminilayi Fubara da yunkurin rushe gidajen majalisar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel