Adamawa: Kwastam Ta Kama Jiragen Ruwa Makare da Man Fetur Za a Kai Kasashen Waje
- Hukumar hana fasa kwauri reshen jihar Adamawa/Taraba ta kama lita 12,435 na fetur a hanyar da za a kai shi Cameroon
- Haka zalika, hukumar ta kuma kama jarkoki 61 dauke da man fetur a hanyar ruwa ta Isalu Creek Badagry za a kai shi Benin
- Wannan dai na zuwa ne yayin da kasar ke fama da wahalar karancin fetur, da kuma yunkurin hukumar Kwastam na dakile fasa kwauri
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Hukumar hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS) reshen jihar Adamawa/Taraba ta ce ta damke lita 12,435 na Premium Motor Spirit (man fetur) wanda kudinsa ya kai Naira miliyan 10.8.
Kwastam ta kama masu safarar fetur
Shugaban hukumar Kwastam na yankin, Bashir Garba-Bature ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Yola, jaridar Vanguard ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewarsa, kayayyakin da aka kama sun hada da jarkoki 491 masu girman lita 25 da guda 8 masu girman lita 20 na fetur, inda ya ce an kama man ne a garin Mubi da ke kan hanyar zuwa Jamhuriyar Cameroon.
"Jami'an hukumar a yayin da suke sintirin hana fasa kwauri a kan yankunan iyakokin kasa, sun ci karo da masu safarar man fetur har sau biyar a hanyarsu ta zuwa Jamhuriyar Kamaru."
- A cewar Bashir Garba-Bature.
Kwastam na neman hadin kan jama'a
Ya ba da tabbacin cewa rundunar za ta ci gaba da yaki da matsalar fasa-kwauri, yana mai cewa: “Mun tura jami’an mu muhimman wurare domin dakile matsalar."
The Guardian ta ruwaito Bature ya nemi hadin kai, fahimtar juna da taimakekeniya daga masu ruwa da tsaki kamar kafafen yada labarai, sauran jami’an tsaro da ‘yan kasa masu kishi.
Ya yi nuni da cewa ta haka ne kawai Najeriy za ta yi nasa wajen ganin an kawo karshen matsalar fasa kwauri ta barauniyar hanya a kasar.
An kama jiragen ruwa dauke da fetur
A wani makamancin labarin, hukumar Kwastam ta kama buhuhuna 177 da jarkoki 61 dauke da man fetur a hanyar ruwa ta Isalu Creek Badagry kan hanyar Jamhuriyar Benin.
Shugaban shiyya na hukumar Kwastam, Kwanturola Paul Bamisaiye, ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a, 10 ga Mayu, 2024 kuma aka wallafa a shafin hukumar na Twitter.
Hukuncin kisa ga masu safara kwayoyi
A wani labarin, mun ruwaito maku majalisar dattawan Najeriya ta zartar da wani kudurin doka da ya ba da damar yanke hukuncin kisa ga masu safara miyagun kwayoyi.
Majalisar ta yi nuni da ce dokar za ta taimaka wajen kawo karshen sha da fataucin miyagun kwayoyi yayin da kuma Sanata Adams Oshiomhole ya nemi majalisar ta yi taka tsantsan.
Asali: Legit.ng