Atiku Bagudu Ya Faɗi Abin da 'Yan Siyasa Ke Son Yi Shekaru da Dama da Tinubu Ya Aiwatar
- Ministan Kasafi a Najeriya, Atiku Bagudu ya ce matakan da Shugaba Bola Tinubu ya ke dauka suna kan hanya
- Bagudu ya ce cire tallafin mai na daga cikin matakan da 'yan takara da dama ke son dauka amma Tinubu ya aiwatar da su
- Ya ce irin waɗannan matakan za su kawo ci gaba wanda ya kamata a dauka tun shekaru da dama da suka gabata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Ministan kasafi da tsare-tsare, Atiku Bagudu ya yabawa matakan da Bola Tinubu ya dauka a Najeriya.
Bagudu ya ce matakin cire tallafin mai da Tinubu ya yi, ya aiwatar da abin da ya kamata a yi shekaru da dama da suka wuce.
Bagudu ya ce Tinubu ya yi fice
Tsohon dan Majalisar Tarayya ya ce abin da sauran shugabanni da 'yan takara suke son yi ne suka gagara Tinubu ya aiwatar a lokaci guda.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon gwamnan Kebbi ya yabawa Tinubu kan irin kokarin da ya yi a cikin watanni 11 kacal da ya yi a kan mulki, cewar Premium Times.
"Tun farko Tinubu ya nuna jarumta wurin daukar matakan da sauran 'yan takara ke son dauka wanda shi ne cire tallafin mai."
"Wannan ba lamari ba ne na zarge-zarge da neman wanda za a daurawa laifi, Tinubu ya dauki matakin ne saboda bai son zargin kowa."
"Amma wasu suna jinkirin daukar matakin da sauran tsare-tsare wanda ya kamata a dauka shekaru aru-aru da suka gabata."
- Atiku Bagudu
Bagudu ya ce Tinubu zai inganta Najeriya
Bagudu ya ce Tinubu ya dauki matakan ne duk ya sanin cewa za a shiga wani hali amma saboda karfin hali ya kaddamar da su domin inganta Najeriya.
Ya ce an yi kokarin samar da wasu hanyoyi da za su rage matsalolin da aka shiga wanda suka saka jama'a a halin kunci sanadin cire tallafi.
Ministan ya ce a kullum Najeriya na kwantanta kanta da Brazil da sauran ƙasashe, sun dade da daukar irin wadannan matakai shekaru da dama da suka wuce.
Bagudu ya magantu kan El-Rufai
Kun ji cewa Ministan kasafin kudi a Najeriya, Atiku Bagudu ya ce ba laifin Shugaba Bola Tinubu bane don Majalisa ta ki sahhalewa Nasir El-Rufai ya zama Minista.
Bagudu ya ce Tinubu ya cika alkawari wajen mika sunan El-Rufai a jerin ministocinsa da ya nemi Majalisar ta tantance don yin aiki tare dashi.
Asali: Legit.ng