2023: Jerin Kananan Hukumomi 30 da Suka Fi Samun Kudi Daga Tarayya a Watanni 12
Abuja - A tsarin mulki da dokar kasa, ana raba kudin tarayya daga asusun hadaka na FAAC ne tsakanin tarayya da Abuja, jihohi da kananan hukumomi.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A rahotonmu, mun tattaro kananan hukumomin da suka fi samun kudi daga FAAC a 2023.
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Kason kananan hukumomin Legas a FAAC
StatiSense ta kawo alkaluman kason da kananan hukumomin da suka fi yawan al’umma suka samu a duka watanni 12 na bara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayanan da aka fitar sun nuna kason Alimosho da ke jihar Legas ya zarce kowace karamar hukuma da sama da Naira biliyan uku.
A jerin kananan hukumomi 30 na farko da suka fi samun katso mai tsoka, kusan 20 duka sun fito daga Legas a Kudu maso yamma.
Kananan hukumomin na Legas kamar Mushin, Oshodi da sauransu sun samu abin da ya kusa kai Naira biliyan 150 daga FAAC.
FAAC: Kananan hukumomin Abuja sun samu N50bn
Akwai kananan hukumomi shida daga birnin tarayya Abuja da suka samu sama da Naira biliyan 50 daga Junairu zuwa Disamba.
Manyan kananan hukumoi daga Kudu maso kudu; Fatakwal da Obio/Akpor sun samu Naira biliyan 12.5, dukkansu suna Ribas ne.
Jihohi da dama sun dogara ne da FAAC, karamar hukumar Nasarawa da ke Kano ta shiga jerin domin ta karbi Naira biliyan 5.45.
A Arewa akwai karamar hukumar Bauchi da ke cikin birnin Bauchi, ita kadai ce a wannan jeri daga yankin Arewa maso gabashin kasar.
1 Lagos, Alimosho: ₦14.36bn
2 FCT: Abuja Municipal: ₦11.51bn
3 Lagos, Ajeromi/Ife: ₦10.94bn
4 Lagos, Kosofe: ₦10.77bn
5 Lagos, Mushin: ₦10.60bn
6 Lagos, Oshodi/Isolo: ₦10.54bn
7 Lagos, Ojo: ₦10.43bn
8 Lagos, Ikorodu: ₦10.21bn
9 Lagos, Surulere: ₦9.91bn
10 Lagos, Agege: ₦9.67bn
11 Lagos, Ifako/Ijaye: ₦9.50bn
12 Lagos, Somolu: ₦9.33bn
13 Lagos, Ikeja: ₦8.89bn
14 Lagos, Eti-Osa: ₦8.89bn
15 Lagos, Amuwo-Odofin: ₦8.85bn
16 Lagos, Lag Mainland: ₦8.83bn
17 Lagos, Badagry: ₦8.54bn
18 FCT, Bwari: ₦8.44bn
19 Lagos, Apapa: ₦8.28bn
20 Lagos, Epe: ₦8.23bn
21 Lagos, Lagos Island: ₦8.22bn
22 FCT, Gwagwalada: ₦7.96bn
23 Lagos, Ibeju-Lekki: ₦7.74bn
24 FCT, Kwali: ₦7.73bn
25 FCT, Kuje: ₦7.71bn
26 FCT, Abaji: ₦7.36bn
27 Rivers, PortHarcourt: ₦6.51bn
28 Rivers, Obio/Akpor: ₦5.99bn
29 Kano, Nasarawa: ₦5.45bn
30 Bauchi, Bauchi: ₦5.39bn
Raddin Shettima ga shugaba Tinubu
Ana da labari cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ba zai ji dadin wasu kalamai da Kashim Shettima ya yi ba.
Na biyu a Najeriyan ya maida martani kan wasu kalaman 'dan takaran adawan bayan ya ba da shawarar koyi da shugaban Argentina.
Asali: Legit.ng