Tinubu Ya Tausaya, Ya Dakakar da Tsarin Biyan Harajin 0.5% da CBN Ya Kawo
- Yayin da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya kakaba harajin 0.5% ga 'yan Najeriya, Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da shi
- Tinubu ya koka kan yadda aka kawo tsarin a dai-dai lokacin da 'yan kasar ke cikin wani irin yanayi na kuncin rayuwa
- Wannan na zuwa ne bayan babban bankin CBN ya kawo sabon tsarin biyan harajin 0.5% kan hada-hadar kudi a bankuna
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Shugaban kasa, Bola Tinubu ya dakatar da biyan harajin tsaron yanar gizo a Najeriya.
Tinubu ya dauki matakin ne bayan Babban Bankin Najeriya (CBN) ya kawo tsarin biyan harajin 0.5% kan masu tura kudi bankuna.
TABLE OF CONTENTS
Tinubu ya damu da halin da ake ciki
Shugaban ya ce ya damu da halin da 'yan ƙasar ke ciki kuma ba zai bari a kara musu wata wahala ba, cewar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kuma ba da umarnin yin garambawul kan tsarin wanda 'yan Najeriya da dama suka yi fatali da shi.
Har ila yau, Tinubu bai ji dadin yadda aka kawo tsarin a dai-dai wannan lokaci ba inda ya bukaci a sake duba kan tsarin.
Wata majiya ta tabbatar da cewa shugaban bai son a dauki gwamnatinsa wacce ba ta da tausayi musanmman a wannan lokaci.
Tinubu ya dakatar da tsarin CBN
"Tinubu ba ya Najeriya lokacin da aka kawo sabuwar dokar, kuma yana gudun ka da a kwatanta gwamnatinsa da rashin tausayi."
"A yanzu haka CBN ya dakatar da fara diban kudin daga bankunan mutane, wannan shi ke nuna Tinubu yana da tausayi kuma bai son karin wahala ga 'yan ƙasar."
"Tuni ya umarci sake duba kan tsarin dokar wanda mafi yawan 'yan Najeriya suka nuna damuwa a kai."
- Cewar majiyar
CBN ya magantu kan tsarin biyan haraji
Kun ji cewa Babban Bankin Najeriya, CBN ya yi karin haske kan wadanda sabon tsarin biyan harajin 0.5% ya shafa.
Bankin ya lissafi hada-hadar kudi 16 da sabon tsarin ba zai shafa ba wanda ya haɗa da kudin albashi da karba ko biyan bashi.
Asali: Legit.ng