Ba Laifin Tinubu Bane Don Majalisa Ta Ki Sahhalewa El-Rufai Ya Zama Minista, Bagudu

Ba Laifin Tinubu Bane Don Majalisa Ta Ki Sahhalewa El-Rufai Ya Zama Minista, Bagudu

  • Minsitan kasafin kudi da tsara tattalin arziki ya tabo batun da ya shafi kin amincewa da El-Rufai cikin ministocin Tinubu
  • A cewarsa hakkin majalisa ne amincewar, don haka ba za a ga laifin Tinubu wajen kin amincewar majalisar
  • Kundin tsarin mulkin Najeriya ya ba majalisar dattawa damar tantancewa tare da duba nagartar ministoci kafin amincewa dasu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

FCT, Abuja - Ministan kasafin kudi da tsara tattalin arzikin Najeriya, Atiku Bagudu ya ce, ba laifin Shugaba Bola Ahmad Tinubu bane don majalisar kasa ta ki sahhalewa Nasir El-Rufai ya zama minista a gwamnatin nan.

A cewar Bagudu, Tinubu ya cika alkawari wajen mika sunan El-Rufai a jerin ministocinsa da ya nemi majalisar ta tantance don yin aiki tare dashi.

Ya bayyana cewa, majalisar ce ta ga dacewar kin amincewa da El-Rufai tare da tabbatar dashi a matsayin ministan, rahoton Premium Times.

Kara karanta wannan

Matakai 5 da Gwamnatin Tinubu ta dauka da suka jefa ‘yan Najeriya a wahalar rayuwa

Babu hannun Tinubu wajen hana El-Rufai minista, Bagudu
Ba laifin Tinubu bane hana El-Rufai minista, Bagudu | Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Nasir El-Rufai
Asali: Facebook

Ba laifin Tinubu bane rashin amincewa da Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake tattaunawa da jaridar, ya ce tsarin demokradiyya da kundin tsarin kasar ne ya ba majalisar ikon tantancewa da amincewa da nagartar ministoci.

Ya kara da cewa:

"Shugaban kasa bai da wani katabus a kudin tsarin mulkin kasa ya yi wani abu. Hakan daidai ne? Amma haka aka tsara dokar."

Yadda El-Rufai ya yi kokari a kamfen Tinubu

A lokacin gangamin neman zaben Tinubu, El-Rufai na daga cikin wadanda suka yi ruwa suka yi tsaki wajen tattabar da nasarar jam'iyyar APC a zaben 2023.

Kafin zaben, Tinubu ya bayyana rokonsa ga El-Rufai a idon duniya, inda yace yana sha'awar aiki dashi idan ya zama shugaban kasa.

A watan Agustan bara ne aka mika sunan El-Rufai cikin jerin ministoci, amma majalisa ta ki amincewa da shi a matsayin wadanda za su yi aiki da Tinubu.

Kara karanta wannan

Rayuwa za ta yi sauki kuma abinci zai wadata a mulkina, Tinubu ya dauki alkawari

Babu wata matsala tsakanin El-Rufai da Tinubu

A bangare guda, jigon jam'iyyar APC a jihar Plateau, Podar Yiljwan Johnson ya magantu kan alakar da ke tsakanin Shugaba Bola Tinubu da Nasir El-Rufai.

Johnson ya ce babu wata matsala tsakanin Tinubu da Nasir El-Rufai kamar yadda ake zargi a wasu bangarori.

Sai dai, har yanzu Shugaba Tinubu ko El-Rufai babu wanda ya bayyana alakar da ake da ita a tsakanin juna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.