Shehi Ya Aikawa Tinubu da Malamai Sako Kan Wahalar Rayuwa da Ake Ciki

Shehi Ya Aikawa Tinubu da Malamai Sako Kan Wahalar Rayuwa da Ake Ciki

  • Sheikh Adamu Muhammad Dokoro a wajen wani karatu da yake yi a Gombe, ya fadakar da masu mulki a Najeriya
  • Babban malamin na addinin musulunci ya ce mutane suna cikin kwa-kwa, ya bukaci bola Tinubu ya tausayawa jama’a
  • A jawabin da ya yi a majalisin karatun, Sheikh Dokoro ya ce malaman da suka tallata APC su ankarar da shugabanni

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Gombe - Sheikh Adamu Muhammad Dokoro ya sake fitowa ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta duba halin da al’ummarta suke ciki.

Adamu Muhammad Dokoro yana cikin malamai da suka saba fadakar da masu mulki game da yanayin da talakawa suka samu kansu.

Tinubu: Sheikh Adamu Dokoro
Sheikh Adamu Dokoro ya fadawa Tinubu ana wahala a Najeriya Hoto: hausaloaded.com, @Dolusegun (X)
Asali: UGC

Bidiyo: Sakon Sheikh Adamu Dokoro ga Tinubu

Kara karanta wannan

Matakai 5 da Gwamnatin Tinubu ta dauka da suka jefa ‘yan Najeriya a wahalar rayuwa

A wani bidiyo da Malam Mubarak Lawal Ibrahim ya wallafa a Facebook, an ji malamin yana jan hankalin Mai girma Bola Ahmed Tinubu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sheikh Adamu Muhammad Dokoro ya ce a hakikanin gaskiya, mutane suna shan wahala, shekara kusan guda kenan da yin canji gwamnati.

Malamin mai shekaru 60 ya bukaci masu mulki su tausayawa jama’an da suke jagoranta, ya nemi Bola Tinubu ya tuna da ranar mutuwa.

A fassarawa Tinubu sakon Sheikh Dokoro

A bidiyon, Sheikh Dokoro ya yi magana da harshen Hausa, yake cewa ba za a rasa wadanda za su fassarawa Bola Tinubu kalamansa ba.

Dokoro wanda ya yi suna a jihar Gombe da kewaye, ya ce akwai wadanda aikinsu shi ne bibiyar maganganun da malaman addini suke yi.

Malamai su fadawa Tinubu ana shan wahala

Lokacin yakin zabe, wasu malamai sun goyi bayan Tinubu-Shettima, Sheikh Dokoro ya nemi malaman su jawo hankalin shugaban kasar.

Kara karanta wannan

"Ba za su iya ba": Sanata Ibrahim ya jero ministocin da ya kamata Bola Tinubu ya kora

“Kuma muna kira ga malaman da suka yi kamfen dinnan, su ma su je suyi magana yanzu.”
“Malaman da suka fito suka yi kamfe kiri-kiri, su ma su je suyi magana.”
"Muna shan wahala, Malam Tinubu muna shan wahala a tuna. Maganar gaskiya ce malam."
“Malam Tinubu muna shan wahala, kuma a tuna ranar mutuwa. Ni ba zan same shi ba ne, amma da zan same shi da na yi magana.”

- Sheikh Adamu Muhammad Dokoro

A karshe, Sheikh Adam Dokoro ya roki Allah SWT ya cusa tausayi a ran masu mulkin domin su gama lafiya ba su gama da talaka ba.

Tinubu ya kawowa talaka sauki?

Tun daga cire tallafi da wahalar man fetur, ana da labarin yadda Bola Ahmed Tinubu ya fara gasawa jama’a aya a hannu a bangarori da yawa.

Maimakon a samu sauki bayan tafiyar Muhammadu Buhari, har yau talaka bai samu saukin rayuwa ba, ana kara shiga cikin matsin lamba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng