Manyan Janar 29 sun yi Ritaya daga Gidan Soja Ana Tsaka da Rashin Tsaro

Manyan Janar 29 sun yi Ritaya daga Gidan Soja Ana Tsaka da Rashin Tsaro

  • Wasu manya-manyan jami’an sojojin kasar nan guda 29 sun yi ritaya bayan kamamala aikin kare rayukan al'umma da rundunar sojojin Najeriya
  • Wannan na zuwa ne a da-dai lokacin da ake kara fama da matsalolin tsaro a sassan Najeriya, musamman a Arewa ciki har da Zamfara da Katsina
  • Manyan jami’an rundunar sojojin da suka yi ritaya sun hada da Manjo Janar guda 19 da Brigadiya Janar guda 10, kuma bayar da shawarar kara kaimi

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kaduna-Wasu manya-manyan jami’an sojin kasar nan guda 29 sun yi ritaya bayan kammala aiki da rundunar sojojin Najeriya.

Kara karanta wannan

Naira ta koma gidan jiya, kudin Najeriya ya dawo mafi rashin daraja a duniya

Wannan na zuwa ne a da-dai lokacin da ake kara fama da matsalolin tsaro a sassan Najeriya, musamman a Arewa da ake kai munanan hare-hare.

Rundunar sojin Najeriya
Manyan jami'an soji 29 sun yi ritaya Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

Premium times ta tattaro cewa daga wadanda suka kammala aikin akwai Manjo Janar guda 19 da Brigadiya Janar guda 10.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojoji na ganin za a magance rashin tsaro

Manjo Janar, Victor Ezugwu da ya yi magana a madadin wadanda suka ajiye aikin ya bayyana yakinin cewa za a iya kawo karshen matsalar tsaron dake addabar kasar nan.

Ya kara da cewa nasara za ta tabbata idan har an samu nasarar kafa sashin sojojin sama a rundunar ta hanyar karfafa hanyoyin samun bayanan sirri, kamar yadda Channels television ta wallafa.

Manjo Janar Victor Ezugwu ya shawarci sojojin su tashi tsaye wajen yakar 'yan ta’addar da ke kawo tarnaki a sassan Najeriya.

Kara karanta wannan

An zargi wani jami'in KEDCO da kashe abokinsa saboda abin duniya

Ya shawarci jami’an rundunar sojojin su zama kula da karfafa dabarun sanin makiyansu, da kaucewa kwantan bauna domin tsira da rayukansu.

Sojoji sun ceto dalibar Chibok

A baya kun ji cewa rundunar sojojin Najeriya ta samu ceto daya daga daliban Chibok da aka sace shekaru 10 da suka gabata, tare da mika ta ga gwamnatin jijar Borno.

An yi nasarar ceto Lydia Simon da yaranta uku daga hannun ‘yan boko haram din da suka sace ta da wasu dalibai da dama a makarantar Chibok dake Borno.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.