InnalilLahi: 'Yan bindiga Sun Bindige Ma'aikacin FIRS a Tsakiyar Birnin Abuja
- An shiga wani irin yanayi bayan wasu 'yan bindiga sun hallaka babban ma'aikacin hukumar FIRS a tsakiyar birnin Abuja
- Maharan sun farmaki matashin ne mai suna Khalid Bichi a Maitama bayan ya fito neman abinci da misalin karfe 9:00 na dare
- Lamarin ya faru ne da daren jiya Juma'a 10 ga watan Mayu inda aka sanar da mutuwarsa a wani babban asibiti da ke birnin
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Wasu 'yan bindiga sun farmaki wani matashi a tsakiyar birnin Abuja inda suka yi ajalinsa.
Maharan sun biyo matashin mai suna Khalid Bichi a Maitama inda suka yi ta harbinsa sai da ya mutu.
Yaushe 'yan bindiga suka hallaka matashin?
Marigayin wanda ma'aikacin hukumar FIRS ne ya fito ne domin siyan abinci a Maitama da misalin karfe 9:00 na dare.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lamarin ya faru ne a daren jiya Juma'a 10 ga watan Mayu yayin da aka kwashe shi zuwa babban asibiti domin ba shi kulawa, cewar Punch.
Daga bisani bayan kai shi asibitin likita ya tabbatar da mutuwarsa nan take bayan bincike na musamman.
An sanar da lokacin jana'izar matashin
Rahoton Zagazola Makama ya tabbatar da cewa marigayin yana da alaka da manyan 'yan siyasa a kasar.
Za a yi sallar jana'izarsa da misalin karfe 1:30 na rana bayan sallar Azahar a babban masallacin Abuja a yau Asabar 11 ga watan Mayu.
A cikin kwanakin nan birnin Abuja na fama da hare-haren 'yan bindiga da kuma fashi wanda ya jefa al'umma cikin tsoro.
'Yan bindiga sun hallaka mutum 30
A wani labarin, kun ji cewa 'Yan bindiga sun kai farmaki kauyuka biyu da aka sansu da sana'ar noma a jihar Zamfara inda suka kashe manoma aƙalla 30.
Rahotanni sun tabbatar da cewa daga cikin waɗanda ƴan bindigar suka kashe har da babban malamin addinin Musulunci, Mallam Makwashi Maradun Mai Jan Baki.
Jihar Zamfara na daga cikin jihohin Arewacin Najeriya da suka fi fama da matsalar tsaro musamman a yankunan karkara.
Asali: Legit.ng