"Babu Tausayi": Ministan Buhari Ya Fadi Yadda Aka Yi Watsi da Shi a Asibiti Kan N80,000
- Tsohon Ministan wasanni, Solomon Dalung ya bayyana yadda ya tsinci kansa a asibiti babu kulawa har awanni hudu
- Dalung ya ce an yi watsi da shi a asibitin Jos fiye da awanni hudu saboda bai biya kudin dubiya N80,000 ba kacal
- Kwamred Dalung ya ce bai san inda ya ke ba tsawon wannan lokaci har sai da ya farfaɗo sannan ya biya kudin aka duba shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Plateau - Tsohon Ministan wasanni a mulkin Muhammadu Buhari ya koka kan abin da ya faru da shi a asibiti.
Solomon Dalung ya ce an yi watsi da shi a asibitin Jos kan N80,000 kacal wanda ya shafe tsawon awanni a asibitin.
Dalung ya shiga wani yanayi a asibiti
Dalung ya bayyana haka ne a shafinsa na X a jiya Juma'a 10 ga watan Mayu inda ya koka kan rashin tausayin jama'a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce an kawo shi asibitin a ranar Laraba inda jim kadan bayan likita ya duba shi kawai sai ya rasa inda hankalinsa ya ke.
Tsohon Ministan ya ce ya shafe awanni hudu ba a duba shi ba saboda rashin biyan kudin har sai da ya farfaɗo ya tura su.
Dalung ya koka da rashin tausayi
"An kawo ni asibiti a ranar Laraba amma na shiga wani yanayi bansan inda na ke ba bayan likita ya mini tambayoyi."
"An kai ni dakin kula da marasa lafiya na gaggawa fiye da awanni hudu ba a duba ni ba har sai da na farfaɗo sannan na tura musu kudin suka duba ni."
"Bayan haka na sake shiga yanayin har na awanni bakwai, bayan kwawani uku an sallame ni yanzu ina samun sauki."
- Solomon Dalung
Dalungi ya ce idan da bai farfaɗo ya biya kudin ba da yanzu marigayi za a kira shi inda ya ce 'yan Najeriya da dama sun tsinci kansu a wannan hali, ina tausayin mutane ya ke?.
Dalung ya magantu kan mukin Buhari
Kun ji cewa Tsohon Ministan wasanni, Solomon Dalung ya ce tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari yana rayuwa cikin dana-sani a yanzu haka.
Dalung wanda ya yi aiki a gwamnatin Buhari ya kuma yi zargin cewa gwamnatin da ta shude ta kasa cika alkawuran da ta dauka wa Najeriya.
Asali: Legit.ng