Naira Ta Koma Gidan Jiya, Kudin Najeriya Ya Dawo Mafi Rashin Daraja a Duniya

Naira Ta Koma Gidan Jiya, Kudin Najeriya Ya Dawo Mafi Rashin Daraja a Duniya

  • Idan mutum ya kai Dala kauwa a yau, zai iya samun N1,468 wanda ya nuna kudin kasar ya sake karyewa sosai a yanzu
  • A yau babu kudin kasar da ba ta daraja irin Naira duk da kokarin da sabon gwamnan CBN yake yi bayan nada shi
  • Akwai karancin daloli a kasuwannin bayan fage da kuma bankuna, wannan ya tilasta faduwar kimar Naira a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Maganar da ake yi, Naira ta cigaba da ruguzowa a teburin darajar kudin kasashen duniya bayan hobbasar kwanakin baya.

Masana tattalin arziki sun ce kudin Najeriyan yana cikin wadanda suka rasa darajarsu a shekarar nan, ya bar mummunan tarihi.

Naira
Naira ta koma mummunan matsayinta na rashin daraja a duniya Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Rahoton Bloomberg ya tabbatar da cewa a yanzu Naira ne kudin da ya fi kowane rashin kima da daraja a kudin kasashen duniya.

Kara karanta wannan

Rayuwa za ta yi sauki kuma abinci zai wadata a mulkina, Tinubu ya dauki alkawari

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nawa Naira take a kan Dala yau?

Kudin Najeriyan na Naira ya fado sosai kan Dala inda ake saida kowace $1 a 1,466.31.

Masu bibiyar hawa da saukar kudin kasar za su fahimci cewa rabon da Naira ta karye haka a kasuwannin canji tun 20 ga Maris.

Za a iya cewa abin da ya jawo faduwar Nairar shi ne zuwa ranar Alhamis, $84m kadai ake da shi da za a iya hada-hada da su a kasar.

A tsakiyar makon nan kuwa, akwai dalolin da sun ribanya wannan adadi a kasuwa da banki.

Naira tayi tashin kumfar teku

Punch ta ce faduwar da Naira tayi yana zuwa ne kwanaki kadan bayan Yemi Cordoso ya ce kudin kasar ya fi na kowace kasa abin kirki.

A watan Maris sai da aka canza dala a kan N1600-N1800 a kasuwannin canji da bankuna, yanayin da ake tsoron zai iya maimaituwa yau.

Kara karanta wannan

Majalisar wakilai ta ki daukar matsaya kan harajin tsaron yanar gizo, 'dan majalisa ya koka

Mecece makomar Naira nan gaba?

Hasashen da Razia Khan ta yi shi ne zuwa karshen watan nan, za a samu karin bukatar daloli, wannan zai sake nakasa kimar Naira.

Kudin Zambia na kwacha da Cedi na kasar Ghana suna cikin masu bin Naira a sahun baya.

Naira: Wani mataki CBN zai dauka?

Wannan hali da aka shiga zai iya matsawa bankin CBN lamba wajen daga darajar ruwa, wanda hakan zai taba masu neman bashi.

Ana da labarin yadda ‘yan adawa suka soki wannan matsaya da CBN ya dauka ganin cewa ana bukatar samar da ayyukan yi a kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng