Hukumar Kwastam Ta Kama Na’urorin Kirifto da Kudin Ganye a Lagos

Hukumar Kwastam Ta Kama Na’urorin Kirifto da Kudin Ganye a Lagos

  • Hukumar kwastam ta kasa reshen jihar Lagos ta sanar da abubuwan da ta kama daga watan Janairu zuwa Afrilun shekarar 2024
  • Kwamandan hukumar na jihar Lagos, Charles Orbih ne ya bayyana haka ga manema labarai a jiya Alhamis, 9 ga watan Mayu
  • Sai dai a tattaunawar da Legit ta yi da wani mai harkar kirifto, Aminu Abubakar, ya bayyana cewa kokarin da gwamnati take na dakile harkar ba abu bane mai kyau

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Lagos - Hukumar kwastam ta Najeriya (NCS) ta sanar da abubuwan da ta kama a jihar Lagos daga watan Janairu zuwa Afrilu.

Custom
Hukumar kwastam ta kama kayan da aka shigo dasu ba bisa ka'ida ba. Hoto: Nigerian Customs Service
Asali: Facebook

Kwamandan kwastam a jihar Lagos, Charles Orbih ne ya bayyana lamarin ga manema labarai a jiya Alhamis, 9 ga watan Mayu.

Kara karanta wannan

Sanatoci sun amince da hukuncin kisa kan masu safarar kwayoyi, an samu hatsaniya

Abubuwan da kwastam ta kama

Jaridar the Cable ta ruwaito cewa hukumar ta kama na'urorin kirifto duba biyar da kuɗin bogi dala miliyan 1.2.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton ya tabbatar da cewa hukumar ta kama kayan ne a filin jirgin saman Murtala Muhammad da ke Lagos.

Yadda kwastam ta yi da kayan da aka cafke

Shugaban hukumar ya tabbatar da cewa sun mika dukkan kayayyakin ga hukumomin da suka dace kamar yadda shugabansu na kasa, Bashir Adeniyi ya bada umurni.

Hukumar ta mika rigunan sulke, rigunan soja da sauran makamai ga major janar Muhammad Usman da ke jagorantar rundunar sojoji ta 81 da ke Lagos.

Kudaden bogi kuma hukumar ta mika su ne ga mataimakin kwamandan hukuma mai yaki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) na jihar, Oguzu Moses.

Kokarin kwastam kan karbar haraji

Kara karanta wannan

Yan sanda sun kashe masu garkuwa da mutane, an kwato miliyoyin kudin fansa

Da yake bayyana irin kuɗin harajin da suka samu kuwa, Mista Orbih ya ce sun samar da kudaden shiga ga Najeriya har Naira biliyan 19 daga watan Janairu zuwa Afrilu, rahoton the Guardian.

A cewarsa, hakan yana nuni da cewa an samu karin kudin shiga daga ɓangaren su da kashi 60% idan aka kwatanta da shekararar 2023.

Jawabi daga mai harkar kirifto

A hirar da Legit ta yi da wani matashi mai yin kirifto, Aminu Abubakar ya ce lalle yunkurin toshe harkar zai kara kawo matsala ga tattalin arziki.

Aminu ya labartawa Legit cewa kirifto ta samar da abin yi ga matasa da dama a Najeriya idan aka dakile ta kuma dimbin matasan za su dawo zaman banza.

Ya bada shawari wa gwamnati cewa idan suna kallon wani lamari da zai zama barazana garesu to kamata ya yi su tsaftace harkar ba dakile ta ba.

Kara karanta wannan

"Za mu dauki kwararan matakai kan barayin gwamnati", EFCC

Kwastam da dakatar da sayar da abinci

A wani rahoton, kun ji cewa hukumar kwastam ta ƙasa ta dakatar da aikin siyar da buhunan shinkafa da sauran kayan abinci a farashi mai rahusa ga ƴan Najeriya.

Mai magana da yawun NCS ta kasa, Abdullahi Maiwada ne ya bayyana haka a wata sanarwa ranar Litinin, 26 ga watan Fabrairu, 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng