Kudurin Majalisa: Za a Rika Yankewa Masu Safarar Miyagun Kwayoyi Hukuncin Kisa
- Majalisar dattawa ta zartar da kudurin yanke hukuncin kisa kan wadanda aka samu da laifin safarar miyagun kwayoyi
- An amince da kudirin ne a ranar Alhamis bayan Sanata Tahir Monguno ya gabatar da rahoto a madadin kwamitin shari’a da kwayoyi
- Sai dai Sanata Adams Oshiomhole ya nemi majalisar dattawan da ta yi taka-tsantsan wajen zartar da dokar da ta shafi 'rayuwa da mutuwa'
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Kudirin dokar da ke neman yanke hukuncin kisa kan wadanda aka samu da laifin safarar miyagun kwayoyi ya tsallake karatu na uku a majalisar dattawa.
Majalisar dattawan ta amince da kudirin ne a ranar Alhamis bayan Tahir Monguno, Sanata mai wakiltar Borno ta Arewa, ya gabatar da rahoto a madadin kwamitocin hadin gwiwa kan harkokin shari’a da miyagun kwayoyi.
Majalisa ta kawo kudurin kisa kan kwayoyi
Da yake gabatar da rahoton, Monguno ya ce akwai bukatar karfafa yaki da miyagun kwayoyi a kasar, kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayan gabatar da rahoton, majalisar dattijai ta shiga cikin "kwamiti na bai daya" domin yin bita kan sassan da ke cikin dokar inda wasu sanatoci suka nuna rashin amincewa da hukuncin kisan.
A lokacin da aka kada kuri'a a zauren majalisar, mataimakin majalisar dattawan, Barau Jibrin ya tsallakar da kudurin bayan sanatocin da suka goyi baya suka fi yawa.
Farautar kwayoyi: Sanata bai goyon bayan kisa
Jaridar Vanguard ta ruwaito sanata mai wakiltar Edo ta Arewa, Adams Oshiomhole, ya ce ya kamata majalisar dattawa ta yi taka tsantsan da duk wata doka da ta shafi 'rayuwa'.
"Bai kamata a gaggauta yanke hukunci kan al'amuran da suka shafi rayuwa da mutuwa ba, ya kamata mu yi taka tsantsan."
- Adams Oshiomhole.
Da yake mayar da martani, Jibrin ya ce:
"Ka yi hakuri tsohon shugaban jam'iyyata na kasa, da ka yi kira da a sake duba kudurin tun farko domin hakkinka ne, amma yanzu mun riga da mun zartar da shi."
- Barau Jibrin
Majalisa za ta binciki kwangilar titin Lagos-Calabar
A wani labarin, mun ruwaito maku cewa majalisar wakilai ta fara gudanar da bincike kan kwangilar gina titin Lagos zuwa Calabar.
Majalisar ta yi nuni da cewa ba a bi ka'ida wajen bayar da kwangilar ba kuma ba a nemi amincewar majalisar dokokin tarayya wajen fitar da kudin aikin ba.
Asali: Legit.ng