Jerin Sanatocin da suka fi kawo kudirorin samar da ci gaban kasa

Jerin Sanatocin da suka fi kawo kudirorin samar da ci gaban kasa

A ranar Lahadin da ta gabata ne muka kawo muku jerin Sanatoci 10 da suka shafe shekara guda ba tare da gabatar da kudiri ko guda daya ba da zai kawo ci gaban kasa.

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan da kuma tsohon gwamnan Kano, Mallam Ibrahim Shekarau (APC, Kano), na daga cikin jerin sanatoci 10 da suka shafe shekara guda cur ba tare da gabatar da kudiri ko daya ba.

Tabbas sashe na 4 cikin kundin tsarin mulkin kasa da aka yi wa kwaskwarima tun a shekarar 1999, ya rataya wa ‘yan majalisun tarayya nauyin gabatar da kudirorin samar da dokar zaman lafiya, da shugabanci nagari a kasar.

Nauyi na farko da ya rataya a wuyan kowane dan majalisar shi ne gabatar da kudirin doka da zai yi daidai da bukatun al’ummomin da suke wakilta tare da sa ido kan yadda ake tafiyar da al’amura a Ma’aikatu, Cibiyoyi da Hukumomin Gwamnati.

Majalisar Dattawa
Hoto daga Nigerian Senate
Majalisar Dattawa Hoto daga Nigerian Senate
Asali: UGC

A ranar 11 ga watan Yunin 2019 ne aka rantsar da sabuwar Majalisar Dattawa ta 9 a tarihin Najeriya, kuma tun daga wancan lokaci kawo yanzu, an gabatar da kudirori fiye da 450 kamar yadda binciken jaridar Daily Trust ya nuna.

Sai dai sabanin haka akwai tulin Sanatoci da suka sha gabatar da kudirori a zauren majalisar dattawa wanda tuni wasunsu sun samu shiga cikin dokar kasa.

KARANTA KUMA: Matawalle ya rantsar da sabbin mashawarta na musamman 15 a Zamfara

A bangaren gabatar da kudirori mafi yawa, Sanata Yahaha Abdullahi na jam'iyyar APC mai wakiltar shiyyar Kebbi ta Arewa, ya fi duk sa'o'insa yayin da ya gabatar da kudirori fiye da 30.

Sai dai dalilin hakan shi ne yadda kowane kudiri da majalisar wakilai ta gabatar ta hannun ya ke biyo wa.

Wadda ta biyo baya a mataki na biyu ita ce Sanata Stella Oduah (PDP, Anambra), wadda ta gabatar da kudirori 29. Na ukunsu shi ne mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ovie Omo-Agege (APC, Delta) da ya gabatar da kudirori 22.

Mafi akasarin kudirorin da Omo-Agege ya gabata su ne wadanda ke neman a yi wa kundin tsarin mulkin kasa kwaskwarima yayin da ya kasance shugaban kwamitin bitar kundin tsarin mulki.

Sauran 'yan majalisar dattawan da kuma adadin kudirorin da suka gabatar su ne kamar haka:

Sanata Ekwunife Lilian Uche (PDP, Anambra) - 17

Sanata Mohammed Sani Musa (APC, Niger) - 14

Sanata Ifeanyi Patrick Ubah (YPP, Anambra) - 13

Sanata Ali Ndume (APC Borno) - 12

Sanata Istifanus Dung Gyang (PDP, Plateau) - 11

Sanata Gershom Henry Bassey, (PDP, Cross River) - 11

Sanata Olamilekan Adeola (APC, Lagos) - 10

Sanata Buhari Abdulfatai (APC, Oyo) - 9

Sanata Opeyemi Bamidele (APC, Ekiti) - 9

Sanata Ike Ekweremadu (PDP, Enugu) - 9

Sanata Ibrahim Barau Jibrin (APC, Kano) - 8

Sanata Aliyu Sabi Abdullahi (APC, Niger) - 8

Sanata Betty Apiafi (PDP, Rivers) - 8

Sanata Uba Sani (APC, Kaduna) - 7

Sanata Ibikunle Amosun (APC, Ogun) - 7

Sanata Ibrahim Yahaya Oloriegbe (APC, Kwara) - 7

Sanata Kashim Shettima (APC, Borno) - 6

Sanata Bassey Albert Akpan (PDP, Akwa Ibom) - 6

Sanata Abba Patrick Moro (PDP, Benue) - 6

Sanata Muhammad Enagi Bima (APC, Niger) - 5

Sanata Abdullahi Adamu (APC, Nasarawa) - 5

Sanata Sadiq Suleiman Umar (APC, Kwara) - 5

Sanata Theodore Ahamefule Orji (PDP, Abia) - 5

Sanata Tolulope Akinremi Odebiyi (APC, Ogun) - 5

Sanata Joseph Obinna Ogba (PDP, Ebonyi) - 5

Sanata Matthew Urhoghide (PDP, Edo) - 4

Sanata Ayo Patrick Akinyelure (PDP, Ondo) - 4

Sanata Aduda Philip Tanimu (PDP, Abuja) - 4

Sanata Samuel Ominyi Egwu (PDP, Ebonyi) - 4

Sanata Biodun Olujimi (PDP, Ekiti) -4

Sanata Ezenwa Francis Onyewuchi (PDP, Imo) - 4

Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko (APC, Sokoto) - 4

Sanata Teslim Kolawale Folarin (APC, Oyo) - 4

Sanata Barinada Barry Mpigi (PDP, Rivers) - 4

Sanata Abdullahi Gobir (APC, Sokoto) - 3

Sanata Robert Ajayi Boroffice (APC, Ondo) - 3

Sanata Ademola Kola Balogun (PDP, Oyo) - 3

Sanata Ahmad Babba-kaita (APC, Katsina) - 3

Sanata Aishatu Dahiru Ahmed (APC, Adamawa) - 3

Sanata Francis Fadahunsi (PDP, Osun) - 3

Sanata Hassan Mohammed Gusau (PDP, Zamfara) - 3

Sanata Rochas Okorocha (APC, Imo) - 3

Sanata Hezekiah Ayuba Dimka (APC, Plateau) - 3

Sanata Michael Ama Nnachi (PDP, Ebonyi) - 3

Sanata Olubunmi Ayodeji Adetunmbi (APC, Ekiti) - 3

Sanata Ramoni Olalekan Mustapha (APC, Ogun) - 3

Marigayiya Sanata Rose Okoji Oko (PDP, Cross River) - 3

Sanata Suswam Torwua Gabriel (PDP, Benue) - 3

Sanata Yusuf Abubakar Yusuf (APC, Taraba) - 3

Sanata Alhaji Ya’u Sahabi (PDP, Zamfara) - 3

Sanata Francis Alimikhena (APC, Edo) - 3

Sanata Adelere Adeyemi Oriolowo (APC, Osun) - 3

Sanata Surajudeen Ajibola Basiru (APC, Osun) - 3

Sanata Amos Bulus Kilawangs (APC, Gombe) - 2

Sanata Clifford Ordia (PDP, Edo) - 2

Sanata Ibrahim Hadejia (APC, Jigawa) - 2

Sanata Abubakar Kyari (APC, Borno) - 2

Marigayi Sanata Benjamin Uwajumogu (APC, Imo) - 2

Sanata Chukwuka Utazi (PDP, Enugu) - 2

Sanata Danjuma Goje (APC, Gombe) - 2

Sanata Degi-eremienyo Wangagra (APC, Bayelsa) - 2

Sanata Emmanuel Bwacha (PDP, Taraba) - 2

Sanata Enyinnaya Abaribe (PDP, Abia) - 2

Sanata Ibrahim Gaidam (APC, Yobe) - 2

Sanata Jibrin Isah (APC, Kogi) - 2

Santa Kabiru Ibrahim Gaya (APC, Kano) - 2

Sanata Adamu Aliero (APC, Yobe) - 2

Sanata Oluremi Tinubu (APC, Lagos) - 2

Sanata Suleiman Abdu Kwari (APC, Kaduna) - 2

Sanata Binos Dauda Yaroe (PDP, Adamawa) -2

Sanata Halliru Dauda Jika (APC, Bauchi) - 2

Sanata Sabo Mohammed (APC, Jigawa) - 2

Sanata Smart Adeyemi (APC, Kogi) - 2

Sanata Ibrahim Abdullahi Danbaba (PDP, Sokoto)

Sanata Ishaku Elisha cliff Abbo (PDP, Adamawa) - 1

Sanata Akon Etim Eyakenyi (PDP, Akwa Ibom) - 1

Sanata Ashiru Oyelola Yisa (APC, Kwara) - 1

Sanata Bala Ibn Na’allah (APC, Kebbi) - 1

Sanata Bello Mandiya (APC, Katsina) - 1

Sanata Chimaroke Nnamani (PDP, Enugu) - 1

Sanata Danjuma Tella La’ah (PDP, Kaduna) - 1

Sanata Danladi Abdullahi Sankara (APC, Jigawa) - 1

Sanata George Thompson Sekibo (PDP, Rivers) - 1

Sanata Ibrahim Mohammed Bomai (APC, Yobe) - 1

Sanata Lawal Yahaya Gumau (APC, Bauchi) - 1

Sanata Orji Uzor Kalu (APC, Abia) - 1

Sanata Oseni Yakubu (APC Kogi) - 1

Sanata Sandy Ojang Onor (PDP, Cross River) - 1

Sanata Shuaibu Isa Lau (PDP, Taraba) - 1

Sanata James Ebiowou Manager (PDP, Delta) - 1

Sanata Saidu Ahmed Alkali (APC, Gombe) - 1

Sanata Umaru Tanko Almakura (APC, Nasarawa) - 1

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng