Tinubu Ya Sallami Wanda Buhari Ya Naɗa, Ya Maye Gurbinsa da Yaron Wike
- Shugaba Bola Tinubu ya kori wanda tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya nada tare da maye gurbinsa
- Tinubu ya nada Injinya Chukwuemeka Woke a matsayin babban daraktan hukumar Ogun-Osun River Basin a Najeriya
- Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadimin shugaban, Ajuri Ngelale ya fitar a jiya Alhamis 9 ga watan Mayu a Abuja
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya nada Injinya Chukwuemeka Woke babban daraktan hukumar Ogun-Osun River Basin.
Woke babban amini ne ga Ministan Abuja, Nyesom Wike wanda ya ba shi shugaban ma'aikatansa lokacin mulkinsa a jihar Rivers.
Tinubu ya nada yaron Wike muƙami
Hadimin shugaban a bangaren yada labarai, Ajuri Ngelale shi ya tabbatar da haka a shafinsa na Facebook a jiya Alhamis 9 ga watan Mayu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mista Woke ya maye gurbin Olufemi Odumosu wanda tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya nada a 2021 bayan dawowarsa mulki a wa'adi na biyu.
"Woke kwararren Injiniya ne kuma ɗan siyasa, ya mulki karamar hukumar Emohua a jihar Rivers."
"Ya rike shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin jihar Rivers a lokacin mulkin tsohon gwamna, Nyesom Wike na tsawon shekaru."
"Tinubu ya bukaci Woke ya yi aiki tukuru domin samar da ci gaba a bangaren albarkatun ruwa wurin yin aiki da gaskiya."
- Ajuri Ngelale
Tinubu ya jawo shi bayan rabuwa da Fubara
Har ila yau, Woke ya rike muƙamin kwamishinan ayyuka na musamman a gwamnatin Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers.
Sai dai Woke yana daga cikin wadanda suka ajiye mukamansu a gwamnatin bayan an samu matsala tsakanin Wike da gwamna Fubara.
Sanata ya shawarci Tinubu kan wasu Ministoci
A wani labarin, Mamban kwamitin kasafin kuɗi na Majalisar Dattawa, Jimoh Ibrahim, ya buƙaci shugaba Bola Tinubu ya kori wasu daga cikin ministocinsa.
Jimoh Ibrahim ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi kan majalisar ministoci da muƙarraban Tinubu yayin hira da 'yan jaridu.
Sanatan ya ce akwai wadanda suka cancanci a dakatar da su saboda rashin yin katabus a gwamnatin inda ya bukaci a maye gurbinsu.
Asali: Legit.ng