'Yan Bindiga Sun Kai Farmaki a Jami'a, Sun Yi Garkuwa da Dalibai a Jihar Kogi

'Yan Bindiga Sun Kai Farmaki a Jami'a, Sun Yi Garkuwa da Dalibai a Jihar Kogi

  • Rahotanni a safiyar yau sun bayyana cewa wasu 'yan bindiga sun kai hari jami’ar kimiyya da fasaha ta Confluence (CUSTEC) da ke jihar Kogi
  • Wani da abin ya faru a kan idonsa ya shaidawa manema labarai cewa 'yan bindigar sun kai harin a daren Alhamis, kuma sun sace dalibai
  • Shugaban jami'ar CUSTEC, Farfesa Abdulraman Asipita, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin bai fadi adadin daliban da aka sace ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Okene, jihar Kogi - 'Yan bindiga sun kai hari jami’ar kimiyya da fasaha ta Confluence (CUSTEC) da ke garin Osara a Okene, jihar Kogi.

An ruwaito cewa sun yi garkuwa da dalibai da dama a harin da suka kai jami'ar a daren ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

"Tana dauke da kwayoyin cututtuka": Hanyoyin da za ku kori 'Tsaka' daga gidajenku

'Yan bindiga sun kai hari jami'ar jihar Kogi
'Yan bindiga sun yi garkuwa da dalibai a wata jami'ar jihar Kogi. Hoto: Custechng
Asali: Facebook

Wani da abin ya faru a kan idonsa ya shaidawa jaridar Daily Trust cewa ‘yan bindigar sun kai farmaki jami’ar ne da misalin karfe 9:00 na dare.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda 'yan bindigar suka kai hari a jami'a

Majiyar ta ce ‘yan bindigan sun shigo ta cikin daji kuma suka shiga ajujuwan da dalibai ke karatu tare da fara yin harbi kan mai uwa da wabi.

Ya ce akalla ajujuwa uku 'yan bindigar suka farmaka, inda suka tasa keyar daliban dake ciki yayin da daliban sauran ajujuwan suka ranta a na kare.

“An dan yi musayar wuta tsakanin 'yan banga, masu gadi da kuma su 'yan bindigar a bakin kofar makarantar, sai dai hakan bai hana su tafiya da daliban ba."

- A cewar majiyar.

A cewar majiyar, daliban na shirye-shiryen jarabawar zangon farko na shekarar da ake sa ran farawa a ranar Litinin 13 ga watan Mayu, lokacin da ‘yan bindigar suka far musu.

Kara karanta wannan

"Za mu karawa abokan hada hadarmu farashi", Masu sana'ar POS

Jami'ar CUSTEC ta tabbatar da kai harin

Wani dalibi, wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya ce shi da wasu abokan karatunsa sun gudu zuwa daji inda suka boye a can na "fiye da sa'a daya".

Shugaban jami'ar CUSTEC, Farfesa Abdulraman Asipita, ya tabbatar da faruwar lamarin amma bai bayar da cikakken bayani kan adadin daliban da aka sace ba.

Kokarin jin ta bakin kwamishinan ‘yan sandan jihar Kogi Mista Bethrand Onuoha ya ci tura yayin da Cdre Jerry Omodara (mai ritaya), mai ba gwamnan jihar shawara kan harkokin tsaro bai amsa kiran waya ba.

Shafin Ebirablog9ja a Facebook ya wallafa irin barnar da 'yan bindigar suka yi a ajujuwan daliban da kuma kokarin jami'an tsaro.

Daliban jami'a sun yi zanga-zanga a Kano

A wani labarin kuma, mun ruwaito maku daliban Kano da ke karatu a jami'ar Dutse, jihar Jigawa sun gudanar da zanga-zanga a gidan gwamnatin jihar Kano.

An ruwaito daliban sun gudanar da zanga-zangar ne saboda nuna rashin jin dadi kan yadda gwamnatin jihar ta gaza cika alkawarinta na biya masu kudin makaranta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.