InnalilLahi: Tsohon Ɗan Wasan Super Eagles, Tijjani Babangida Ya Yi Hatsari, an Rasa Rai
- An shiga jimami bayan rasuwar kanin fitaccen tsohon dan wasan Najeriya, Tijjani Babangida a jihar Kaduna
- Hatsarin ya faru ne a yau Alhamis 9 ga watan Mayu a kan hanyar Kaduna zuwa Zaria wanda Ibrahim Babangida ya rasa ransa
- Tsohon ɗan wasan, Tijjani da matarsa mai suna Maryam Waziri suna kwance asibiti domin karbar kulawa na musamman
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kaduna - Tsohon ɗan wasan Super Eagles, Tijjani Babangida ya gamu da hatsarin mota a jihar Kaduna.
Hatsarin ya faru ne a yau Alhamis 9 ga watan Mayu a kan hanyar Kaduna zuwa Zaria a jihar.
Kanin Tijjani Babangida ya rasu a hatsarin
BBC Hausa ta tabbatar da cewa hatsarin ya rusa da kanin fitaccen ɗan wasan mai suna Ibrahim Babangida wanda ya rasa ransa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Marigayin shi ma tsohon ɗan wasan Super Eagles ne da ya taka rawar gani a shekarun baya.
Tijjani da matarsa mai suna Maryam Waziri suna asibiti yanzu haka suna karbar kulawa.
Mukamin Tijjani Babangida a Najeriya
Babangida shi ya ke rike da shugabancin kungiyar kwararrun 'yan wasan Najeriya (PFAN), cewar rahoton Punch.
Sakataren kungiyar kuma tsohon ɗan wasan Najeriya, Emmanuel Babayaro ya tabbatar da faruwar hakan a yau Alhamis 9 ga watan Mayu.
"Ya kamata mu saka shugabanmu a cikin addu'a, Tijjani Babangida wanda ya gamu da hatsarin mota a kan hanyar Kaduna zuwa Zaria."
"Kaninsa, Ibrahim Babangida ya rasu nan take inda Tijjani da matarsa aka kwashe su zuwa asibiti."
"Muna addu'ar ubangji ya jikan Ibrahim Babangida ya sa ya huta."
- Emmanuel Babayaro
Ribadu ya tafka babban rashi
A wani labarin, kun ji cewa mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Mallam Nuhu Ribadu ya yi rashin ɗan uwansa, Salihu Ahmadu Ribadu.
Marigayin ya rasu ne a Yola, babban birnin jihar Adamawa a ranar Lahadi, 5 ga watan Mayun 2024 bayan fama da jinya.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aika da tawaga ta musamman domin yi wa Nuhu Ribadu ta'aziyya kan wannan babban rashi da ya yi.
Asali: Legit.ng