Majalisa Ta Amince da Karin Albashi Ga Wasu Ma'aikata, an Fadi Yawan Kuɗin
- Majalisar Dattawa ta amince da kudirin karin albashi ga ma'aikatan shari'a a Najeriya yayin da ake cikin wani halin matsi
- Kudirin da aka gabatar a gaban Majalisar ya tsallake karatu na biyu inda shugaban alkalai zai samu albashin N5.38m a wata
- Sanata Ashiru Yisa daga jihar Kwara ne ya gabatar da kudirin a gaban Majalisar kan inganta albashi da alawus na ma'aikatan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Kudirin da ke neman karin albashi ga alkalai ya tsallake karatu na biyu a Majalisar Dattawa.
Majalisar ta sake karanto kudirin ne a yau Alhamis 9 ga watan Mayu yayin zamanta a birnin Tarayya Abuja.
Za a kara albashin alkalai a Najeriya
Wannan ya biyo bayan yunkurin sake duba karin albashin ma'aikatan shari'a da kuma alawus dinsu a fadin kasar, cewar The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanata Ashiru Yisa daga jihar Kwara wanda shi ne mataimakin shugaban masu rinjaye a Majalisar shi ya gabatar da kudiri, cewar Premium Times.
A ranar 20 fa watan Maris din wannan shekara, Majalisar Wakilai ta gabatar da kudiri domin ba shugaban alkalan Najeriya albashin N5.38m a wata.
Albashin da alkakai za su iya samu
Kudirin har ila yau, ya amince da biyan shugabannin kotunan koli N4.21m yayin da shugaban kotun daukaka kara zai samu N4.48m a wata.
Har ila yau, alkalan kotunan daukaka kara za su samu albashin N3.73n a kowane wata a Najeriya.
Alkalin babbar kotun Tarayya da alkalan manyan kotunan jihohi da kotunan Sharia da Kwastomari da sauransu za su samu N3.53m a wata.
Majalisa ta dauki mataki kan safarar kwayoyi
A wani labarin, mun kawo muku cewa Majalisar Dattawa ta amince da hukuncin kisa kan wadanda aka kama da safarar kwayoyi.
Majalisar ta tabbatar da wannan doka a yau Alhamis 9 ga watan Mayu yayin zamanta a birnin Abuja.
Wannan mataki ya biyo bayan gabatar da rahoto da kwamitin Majalisar a bangaren 'yancin dan Adam da fannin shari'a da kuma NDLEA.
Asali: Legit.ng