Mutane Sun Mutu a Sanadiyyar Hatsarin Iskar Gas a Jihar Lagos
- An samu hatsarin tukunyar iskar gas a yankin Ijebu-Lekki na jihar Lagos wanda ya jawo asarar rayuka da raunata mutane
- Kakakin rundunar'yan sandan jihar, SP Benjamin Hundeyin ya tabbatar da faruwar lamarin tare da bayyana halin da ake ciki
- SP Benjamin Hundeyin bai bayyana sanadiyyar gobarar ba amma yace ana kan binciken gano irin girman asarar dukiya da ta jawo
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Lagos - An samu mummunan hatsarin tukunyar iskar gas a yankin Ijebu da ke jihar Lagos a yammacin Talata.
A sanadiyyar hatsarin, mutane biyu sun rigamu gidan gaskiya yayin da mutane da dama suka jikkata.
Hatsarin ya zo ne biyo bayan samun irinsa a yankin Ajegunle cikin satin da ya wuce wanda ya kona mutane da dama, cewar jaridar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jawabin kakakin 'yan sandan Lagos
Kakakin rundunar 'yan sanda jihar, SP Benjamin Hundeyin ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai.
SP Hundeyin ya tabbatar da cewa hatsarin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane guda biyu, mace da namiji.
Daya daga cikin wadanda suka mutu yar uwar mai shagon da tukunyar iskar gas din take ne daya namijin kuma yazo yin sayayya ne hatsarin ya rista da shi.
A bangaren wadanda suka yi rauni an samu mutum uku da suka jikkata kuma a halin yanzu suna karban magani a asibiti.
Asarar dukiya da hatsarin ya jawo a Lagos
Kakakin 'yan sandan ya kuma tabbatar da cewa shaguna hudu da suke kusa da inda tukunyar gas din ta fashe sun kone kurmus.
Har ila yau ya kara da cewa yanzu haka ana lissafi domin gano adadin asarar da gobarar ta jawo, rahoton jaridar the Cable.
Hatsarin mota ya kashe mutane da dama
A wani rahoton, kun ji cewa an shiga jimami yayin da wata motar bas ta ci karo da babbar mota a kan haryar Legas zuwa Ibadan da safiyar Litinin.
Hatsarin ya faru inda mutane hudu su ka rasa rayukansu yayin da wasu da dama ke karbar magani a asibitin Sagamu da ke Ogun kuma kakakin Hukumar FRSC ta tabbatar da lamarin.
Asali: Legit.ng