N15tr: "Za Mu Binciki Yadda Aka Ba da Kwangilar Titin Lagos Zuwa Calabar", Majalisa
- Majalisar wakilai ta bayyana cewa za ta gudanar da bincike kan yadda aka bayar da kwangilar babbar hanyar Legas zuwa Calabar
- Hon. Austin Achado (APC, Benue) ne ya gabatar da kudirin gaggawa kan aikin ginin a yayin majalisar na yau Alhamis, 9 ga Mayu
- Achado ya zargi gwamnati da kin bin ka'idoji wajen bayar da kwangilar aikin titin mai tsayin kilomita 700 da zai lashe har N15trn
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Majalisar wakilai a ranar Alhamis, 9 ga watan Mayu, ta yanke shawarar gudanar da bincike kan yadda aka bayar da kwangilar babbar hanyar Legas zuwa Calabar.
Majalisar ta cimma wannan matsayar ne bayan da Hon. Austin Achado (APC, Benue) ya gabatar da wani kudiri na gaggawa da ke da muhimmanci ga jama'a.
Jaridar The Nation ta ruwaito majalisar ta bukaci ma’aikatar ayyuka da ta yi mata cikakkun bayani kan hanyoyin da ake bi wajen bayar da kwangilar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An zargi gwamnatin Tinubu da saba ka'ida
Akwai 'yan korafe-korafe da aka yi game da bayar da kwangilar gina titin ga kamfanin Hitech Construction a kan kudi Naira biliyan hudu kowacce kilomita daya.
Gwamnati dai ta sanar da gina titin mai tsayin kilomita 700 a cikin shekaru biyar, kuma zai lashe akalla Naira tiriliyan 15.
Hon. Achado ya sanar da majalisar cewa gwamnatin tarayya ba ta bi ka'ida ba wajen bayar da wannan kwangila ga kamfanin Hitech, Channels TV ta ruwaito wannan.
'Dan majalisar ya kuma kara da cewa hatta ita kanta majalisar dokokin kasar ba ta amince da kudaden da za a yi aikin ba.
Atiku ya kalubalanci gwamnatin Tinubu
Tun da fari, mun ruwaito maku cewa Atiku Abubakar ya zargi gwamnatin Bola Tinubu da rufa-rufa kan bayar da kwangilar titin Lagos-Calabar.
'Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben 2023 ya kuma kalubalanci gwamnatin da ta fitar da bayanan kwangilar kama daga yadda aka nemi kwangilar da kudin da aka bayar.
Ya yi zargin cewa an bayar da kwangilar ba tare da ba wasu kamfanonin damar neman kwangilar aikin ba kamar yadda doka ta sahale.
Asali: Legit.ng