"Yana da Kyau Amma...": Dattawan Arewa Sun Bayyana Matsayarsu Kan Harajin CBN
- Kungiyar Dattawa Arewa ta yi martani kan sabon matakin da Babban Bankin Najeriya, CBN ya kawo na biyan harajin 0.5%
- Kungiyar ta yi fatali da matakin inda ta bukaci gwamnatin kasar ta sake tunani kan lamarin saboda halin da 'yan ƙasar ke ciki a yanzu
- Hakan ya biyo bayan ƙaƙaba harajin 0.5% da bankin ya yi kan 'yan Najeriya yayin tura kudi saboda tsaron yanar gizo a kasar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kaduna - Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) ta bayyana matsayarta kan sabon harajin 0.5% da aka kawo.
Kungiyar ta bayyana cewa tsarin yana da amfani kam amma ta kushe matakin da aka kakabawa jama'a musamman a wannan lokaci.
Matsayar Dattawan Arewa kan harajin CBN
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktan yada labaran kungiyar, Abdul-Azeez Suleiman ya fitar, cewar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abdul-Azeez Suleiman ya ce wannan mataki da babban bankin CBN ya dauka ya saba doka kuma bai dace a wannan lokaci ba.
Kungiyar ta bukaci gwamnati da ta sake duba kan lamarin inda ta nemi kawo hanyoyin sassautawa jama'a a kasar, Daily Post ta tattaro.
Dattawan Arewa sun fadi amfanin tsarin
Yayin da kungiyar ta bayyana amfanin tsaron yanar gizo, ta bukaci yin adalci wurin karin kudin ba tare da wuce gona da iri ba.
Wannan na zuwa ne bayan ƙaƙaba biyan harajin 0.5% na tsaron yanar gizo kan kwastomomin bankuna a Najeriya.
Bankin ya ce daukar matakin ya zama dole domin tabbatar da tsaron yanar gizo da ke cikin hatsari.
Bankin CBN ya kawo sabon haraji
A wani labarin, kun ji cewa Babban Bankin Najeriya, CBN ya kawo wani sabon tsari na biyan harajin 0.5% a Najeriya.
Sai dai daga bisani bankin ya jero hada-hadar kudi 16 da wannan tsari ba zai shafa ba domin wayar da kan 'yan ƙasar.
Wannan mataki da aka kawo bai samu karbuwa ba yayin 'yan ƙasar suka yi ta korafi game da biyan harajin ganin irin halin da suke ciki a yanzu.
Asali: Legit.ng