Rashin Biyan Kudin Makaranta: Daliban Kano Sun Yi Zanga Zanga a Gidan Gwamnati

Rashin Biyan Kudin Makaranta: Daliban Kano Sun Yi Zanga Zanga a Gidan Gwamnati

  • Ana tunanin akalla daliban Kano 3,000 ne da ke karatu a jami'ar tarayya ta Dutse, jihar Jigawa ba su iya sun biya kudin makarantar su ba
  • Daliban sun gudanar da zanga-zanga a gidan gwamnatin Kano inda suke nemi Gwamna Abba Yusuf ya cika alkawarin da gwamnati ta dauka
  • A shekarar 2023, gwamnatin Kano ta yi alkawarin za ta rika biyan 60% na kudin makarantar daliban, wanda har yznzu ba ta biya ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Kano - Daliban jihar Kano da ke karatu a jami’ar tarayya ta Dutse, jihar Jigawa, sun yi zanga-zangar nuna rashin jin dadin gazawar gwamnatin Kano wajen biyan kudin makarantarsu.

Kara karanta wannan

Ba mu yarda a tsige gwamnan Rivers ba, jam'iyyar PDP ta fusata kan kalaman APC

Dalibai sun zargi gwamnatin Kano da gaza biyan kudin makarantarsu
Daliban Kano a jami'ar Dutse sun gudanar da zanga-zanga a gidan gwamnati. Hoto: Sha'aibu Abdulmumini
Asali: Facebook

Daliban wadanda mambobi ne na kungiyar daliban jihar Kano ta kasa (NAKSS), sun ce sama da mutum 3,000 daga cikin su a jami’ar ba a biya wa kudin ba.

Tsakanin gwamnatin Kano da daliban FUD

A yayin zanga-zangar, daliban sun bukaci gwamnatin jihar da ta cika alkawarin da ta yi na biyan kudaden domin ba su samu damar yin jarrabawa, jaridar Premium Times ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugabannin kungiyar daliban jihar (NAKSS) reshen jami'ar Dutse, sun ce ko a shekarar da ta gabata sai da suka biya kudin aka bari suka zana jarabawa.

Sun shaidawa manema labarai cewa gwamnatin Kano ce ta yi alkawarin za ta rika biyan 60% na kudin makarantar daliban bayan cimma matsaya da hukumar jami'ar.

Sai dai shugaban kungiyar daliban na FUD, Umar Korau, ya ce har yanzu gwamnati ba ta biya kudin ba, kimanin watanni takwas kenan.

Kara karanta wannan

An gurfanar da mutumin da ake zargi da safarar makamai ga 'yan bindiga a Kano

Jami'ar FUD ta hana daliban Kano jarabawa

Kwamred Korau ya ce sama da dalibai 3,000 ba su iya biyan kudin makarantar ba, wanda ya zama dalilin yin kira ga gwamnati da ta cika alkawarinta.

Gidan rediyon Premier da ke Kano, ya ruwaito cewa daliban sun zargi gwamnatin jihar Kano da biya wa daliban jami'ar Bayero da na ABU kudin makarantar amma su aka tsame su.

Daliban sun koka da yadda hukumomin jami’ar suka bukaci a biya su kudaden kafin su ba wa daliban damar zana jarabawar zangon farko.

A watan Janairun shekarar da ta gabata ne jami'ar ta sanar da karin kashi 200% na kudaden makaranta.

Abba ya biya 'yan fanshon Kano N5bn

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa Gwamna Abba Yusuf na jihar Kano ya ba da umarnin a biya giratutin Naira biliyan biyar ga 'yan fanshon jihar.

Wannan dai shi ne karo na biyu da gwamnatin Kano ke ware biliyoyin Naira domin biyan tsofaffin ma'aikatan jihar hakkokinsu wanda ta fara a Disambar 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.