'Yan Bindiga Sun Kai Farmaki Makarantar Sakandire a Arewa, Sun Tafka Ɓarna

'Yan Bindiga Sun Kai Farmaki Makarantar Sakandire a Arewa, Sun Tafka Ɓarna

  • Wasu ƴan bindiga da ba a sani ba sun kai hari makarantar sakandire a kauyen Adeke da ke jihar Benuwai ranar Talata da daddare
  • Daraktan yaɗa labarai na cocin katolika a Makurɗi ya tabbatar da kai harin amma ya ce babu abin da ya samu shugaba da ɗaliban makarantar
  • Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar, Catherine Anene, ta ce rahoton kai hari makarantar bai iso gare ta ba zuwa lokacin

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Benue - Miyagun ƴan bindiga sun kai hari makarantar sakandiren Father Angus Frazer Memorial High School da ke ƙauyen Adeke a jihar Benuwai.

Kamar yadda jaridar The Sun ta tattaro labarin, maharan waɗanda ba a san ko su wanene ba sun yi wa mai gadin da ke bakin aiki mummunan rauni a harin ranar Talata da daddare.

Kara karanta wannan

Uba Sani ya fara shirin tashin makarantu sama da 300 a Wwsu yankuna a Kaduna

Sufetan ƴan sanda, IGP Kayode.
Yan bindiga sun kai hari makarantar sakandire da daddare a jihar Benue Hoto: PoliceNG
Asali: Facebook

Daraktan sadarwa na cocin katolika ta Makurɗi, babban birnin jihar Benwaui, Rabaran Moses Iorapuu, ya tabbatar da kai hari makarantar wadda ke ƙarƙashin cocin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An rufe makarantar sakandare a Benue

Rahoton jaridar Tribune Nigeria ya nuna cewa a halin yanzun mahukunta sun kulle makarantar na wucin gadi sakamakon kai harin.

Rabaran Iorapuu ya ce:

"Labari mara daɗi da muke samu daga ɗaya daga cikin makarantun mu ya nuna cewa wasu ƴan bindiga sun kai hari makarantar Angus Frazer Memorial a daren jiya (Talata, 7 ga watan Mayu)."
"Babu abin da ya samu shugaban makarantar, Emmanuel Ogwuche da ɗalibai amma mai gadi ɗaya ya samu rauni yayin harin kuma yanzu haka an kwantar da shi a asibiti."

Wane mataki ƴan sandan Benue suka ɗauka?

Yayin da aka tuntuɓe ta jami'ar hulɗa da jama'a ta rundunar ƴan sandan jihar Benue, Catherine Anene, ta ce har yanzu ba ta samu rahoto kan wannan lamarin ba.

Kara karanta wannan

Majalisa ta ɗauki wasu matakai na ƙawo ƙarshen satar ɗalibai da tsaro a Najeriya

Legit Huasa ta tattaro cewa jihar Benuwai na ɗaya daga cikin wuraren da rikicin makiyaya da manoma ya fi yi wa illa, inda ake zargin makiyaya da lalata amfanin gona.

Majalisa ta ɗauki matakai kan rashin tsaro

A wani rahoto na daban, Majalisar wakilan ta ɗauki wasu matakai da nufin kawo karshen satar ɗalibai a makarantu da dawo da tsaro a Najeriya

Ta umurci kwamitocinta da suka shafi hukumomin tsaro da na tsaro su zauna da hafsoshin tsaron ƙasar nan domin lalubo mafita mai ɗorewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel