An Shiga Fargaba Yayin da 'Yan Banga Suka Bindige Babban Jami'in Ɗan Sanda a Taraba

An Shiga Fargaba Yayin da 'Yan Banga Suka Bindige Babban Jami'in Ɗan Sanda a Taraba

  • Wasu 'yan banga sun kai wani farmaki inda suka yi ajalin wani jami'in dan sanda da ke bakin aiki a jihar Taraba
  • Lamarin ya faru ne a ranar 4 ga watan Mayu a kauyen Sardauna da ke karamar hukumar Gassol a jihar
  • Kwamishinan 'yan sanda, David Iloyanomon shi ya tabbatar da haka inda ya ce sun baza jami'an tsaro domin cafke wanda suka aikata kisan

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Taraba - An shiga jimami bayan wani jami'in dan sanda ya gamu da ajalinsa a jihar Taraba.

Wasu 'yan banga ne suka bindige dan sandan yayin wani farmaki da suka kai a karamar hukumar Gassol.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari kauyen Kaduna, sun kashe mutane da dama

Yan banga sun bindige jami'in dan sanda a Taraba
Wasu 'yan banga sun harbe jami'in dan sanda a jihar Taraba. Hoto: Nigeria Police Force.
Asali: Twitter

Taraba: Yaushe aka hallaka dan sandan?

Lamarin ya faru ne a ranar 4 ga watan Mayu a kauyen Sardauna da ke karamar hukumar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamishinan 'yan sanda a jihar, David Iloyanomon shi ya tabbatar da haka a shafin Facebook inda ya bayyyana marigayin da suna ASP Tapu Godfrey.

David ya ce marigayin na daga cikin jami'an tsaro na musamman masu sintiri a yankin kafin faruwar lamarin.

Ya ce 'yan bangan karkashin jagorancin Ali Dossol ne suka farmaki rundunar wanda hakan ya saka jami'an tsaro gaggawar maida martani.

"Yan banga sun bude wuta inda suka harbi ASP Godfrey a cinya wanda aka kwashe shi zuwa asibitin Sandirde."
"Bayan kai shi asibitin domin ba shi kulawa na musamman, likita ya sanar da cewa dan sandan ya mutu."

- David Iloyanomon

Alkwarin da 'yan sanda suka yi

Kara karanta wannan

Borno: Gwamna Zulum ya tafka babban rashi yayin da hadiminsa ya rasu

David ya sha alwashin cafke dukkan wadanda suke da hannu a kisan inda ya ce sun baza jami'an tsaro.

Ya kuma tura sakon jaje ga iyalan marigayin inda ya yi alkawari ga al'ummar yankin cewa jami'an tsaro za su zakulo wadanda suka aikata kisan.

Tsohon kwamishina ya rasu a Taraba

A wani Labarin, an ji tsohon kwamishinan lafiya a jihar Taraba, Dakta Innocent Vakkai ya riga mu gidan gaskiya.

Marigayin ya rasu ne a ranar Juma'a 3 ga watan Mayu a babban asibitin Tarayya da ke Jalingo bayan fama da jinya.

Tsohon gwamnan jihar, Injiniya Darius Ishaku shi ya tabbatar da haka inda ya tura sakon jaje ga iyalan marigayin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.