Shugaba Bola Tinubu zai Kaddamar da Tashar Tsandauri ta 3 a Arewacin Najeriya

Shugaba Bola Tinubu zai Kaddamar da Tashar Tsandauri ta 3 a Arewacin Najeriya

  • A gobe Alhamis ne Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu zai kaddamar isa jihar Katsina domin kaddamar da tashar tsandauri Funtua
  • Tashar za ta biyo bayan takwarorinta ta Kaduna da aka samar a shekarar 2018, da ta Dala a jihar Kano da aka samar a shekarar 2023
  • Ana samar da tashoshin tsandauri a Arewacin Najeriya domin saukaka shigo da kaya yankin daga kasashen waje ba sai an yada zango a bakin teku ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Katsina-Gwamnatin tarayya za ta kaddamar da tashar tsandauri a Funtua da ke Arewacin jihar Katsina gobe Alhamis.

Tashar tsandaurin jihar Katsina ce za ta zama ta uku a yankin Arewa, inda aka samar da ta farko a jihar Kaduna, ta biyu kuma a jihar Kano.

Kara karanta wannan

"Za mu dauki kwararan matakai kan barayin gwamnati", EFCC

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai kaddamar da tashar tsandauri a Funtua, Katsina Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Gwamnati ta gina tasha a kan tudu

A rahoton da Nigerian Tribune ta wallafa, shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu ne zai kaddamar da tashar tsandaurin a Funtua kamar yadda Rebecca Adamu, mataimakiyar daraktan yada labarai a hukumar kula da shige da ficen jiragen ruwa (NSC) ta bayyana.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta ce wannan gagarumin ci gaba ne a kokarinsu na habaka kasuwanci a kasar nan ta fuskoki da dama.

"Tashar Katsina za ta saukaka kasuwanci," NSC

Shugaban hukumar kula da shige da ficen jiragen ruwa (NSC), Barista Pius Ukeyima Akutah ya bayyana tashar tsandaurin Katsina da gagarumin nasara ta fuskar habaka kasuwanci.

Ya ce daga ci gaban da tashar tsandaurin Funtua za ta kawo akwai saukakawa masu shigo da kaya yankin Arewa da ba sa kusa da teku, sannan za ta rage cunkuso a bakin tekun kasar nan.

Kara karanta wannan

An gurfanar da mutumin da ake zargi da safarar makamai ga 'yan bindiga a Kano

Barista Pius Ukeyima Akutah ya kara da cewa ana sa ran tashar za ta samar da ayyukan yi da karin kudin shiga ga gwamnatocin kasar nan, kamar yadda Punch News ta wallafa.

Gwamnati za ta kaddamar da rancen dalibai

Mun ruwaito muku cewa gwamnatin tarayya ta bayyana za ta tabbatar da kaddamar da shirin ba dalibai rancen kudin karatu na NELFund duk da jinkirin da aka samu.

Sakataren shirin na NELFund, Dr Akintunde Sawyer, ya tunatar da daliban da suka cancanta su gaggauta yin rijista a shafin yanar gizo da aka bude a watan Maris din 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.