Miyagu Sun Tafka Ɓarna, Sun Yi Garkuwa da Fasinjojin Jirgin Ruwa a Najeriya

Miyagu Sun Tafka Ɓarna, Sun Yi Garkuwa da Fasinjojin Jirgin Ruwa a Najeriya

  • Rundunar ƴan sanda ta tabbatar da cewa wasu ƴan fashin teku sun yi garkuwa da mutum bakwai a kogin Onne da ke jihar Ribas
  • Mai magana da yawun ƴan sandan jihar, Grace Iringe-Koko, ta ce lamarin ya faru ne yayin da wani jirgin ruwa ya taso daga Bonny da nufin zuwa Onne
  • Ta ce maharan sun yi wa fasinjojin jirgin fashi kafin daga bisani kuma suka tafi da mutum bakwai zuwa wurin da ba a sani ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Rivers - Rahotanni sun bayyana cewa akalla matafiya bakwai ne aka yi garkuwa da su a tafkin Onne da ke jihar Ribas a Najeriya.

An tatttaro cewa ƴan bindigar sun kai wa matafiyan farmaki ne yayin da suke hanyar zuwa Fatakwal a cikin wani jirgin ruwa ranar Litinin, 6 ga watan Mayu.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka mutum 8 tare da sace manajan banki a Zamfara

Sufetan ƴan sanda na ƙasa, IGP Kayode.
Yan fashin teku sun yi garkuwa da mutum bakwai a wani kogi a jihar Rivers Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Rundunar ƴan sandan jihar Ribas ta tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai ranar Talata, 7 ga watan Mayu, 2024, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jami'ar hulɗa da jama'a ta rundunar ƴan sandan jihar, Grace Iringe-Koko, ta bayyana cewa fasinjoji 20 ne a cikin jirgin ruwan lokacin da ƴan fashin suka tare su.

Rivers: Yadda aka yi garkuwa da matafiya

Ta ce jami'an sojin ruwa sun sanar da rundunar ƴan sanda cewa ƴan bindigan ruwa sun tare wani jirgin ruwa mai ɗauke da mutum 20 kuma sun masu fashi.

A cewarta, daga bisani maharan suka yi awon gaba da mutum bakwai daga cikin fasinjojin zuwa wani wuri da ba a sani ba, Channels tv ta ruwaito.

Kakakin ƴan sandan ta ce lamarin ya faru ne a daidai tafkin Onne yayin matafiyan waɗanda suka taso daga Bonny, ke kan hanyar zuwa Onne.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da wani matashi, Abdullahi ya kashe matarsa kan ƙaramin abu

"Eh haka ne jagoran rundunar sojin ruwa ya sanar da ni cewa ƴan fashin teku sun tare wani jirgin ruwa mai ɗauke da fasinjoji 20 wanda ya taso daga Bonny zuwa Onne.
"Maharan sun tare su a daidai Kogin Onne inda suka masu fashi kana daga bisani suka yi awom gaba da mutum bakwai zuwa wurin da ba a sani ba."

- Grace Iringe-Koko.

Majalisa ta sake dira kan gwamnan Rivers

A wani rahoton kuma kun ji cewa Majalisar dokokin jihar Ribas ta sake bijirewa Gwamna Siminalayi Fubara a karo na uku cikin watanni uku.

Majalisar ta kuma yi barazanar ɗaukar matakai masu tsauri kan gwamnan matuƙar ya ci gaba da sa kafa yana shure dokokin da ta amince da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262