Jerin Kasashe 10 da 'Yan Jarida Ba Su da Cikakken 'Yanci a Duniya

Jerin Kasashe 10 da 'Yan Jarida Ba Su da Cikakken 'Yanci a Duniya

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ranar ƴancin ƴan jarida ta duniya da ake gudanarwa kowace shekara a ranar 3 ga watan Mayu, rana ce ta musamman da aka keɓe domin murnar muhimmancin aikin jarida, ƴancin ƴan jarida, da ƴancin samun bayanai.

Majalisar ɗinkin duniya a yayin babban taron ta na shekara-shekara ta ayyana ranar a watan Disamba na shekarar 1993.

'Yan jarida na fuskantar barazana a wasu kasashe
Akwai kasashen da ake musgunawa 'yan jarida a duniya Hoto: Alex Pena
Asali: Getty Images

Akwai ranar 'yan jarida a duniya

Ranar ta zama abin tunatarwa kan muhimmiyar rawar da aikin jarida da masu yinsa ke takawa wajen inganta dimokuradiyya da bayyana gaskiya a duniya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴancin ƴan jarida yana ba su damar yin bincike tare da kawo rahoto kan abubuwan da suka shafi jama'a ba tare da tsoron fuskantar takura ko barazana ba.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka kwamandan rundunar NSCDC yayin fafatawa a Benue

Sai dai, ba a kowane ƙasashe ba ne ƴan jarida suke da ƴancin gudanar da ayyukansu ba tare da takura ba.

Ƙasashen da ake takurawa ƴan jarida

Jaridar Tribune ta jero ƙasashe 10 waɗanda ƴan jarida ba su da cikakken ƴancin gudanar da ayyukansu.

Ga jerinsu a nan ƙasa:

1. Eritrea

Eritrea na a sahun gaba cikin ƙasashen da ƴan jarida ba su da ƴanci a duniya. Ita ce ƙasa ɗaya tilo a Afirika da babu kafafen yaɗa labarai masu zaman kansu.

Tun lokacin da ƙasar ta samu ƴancin kai, gwamnati ke da cikakken iko kan kafafen yaɗa labarai, yayin da aka rufe gidan jaridu masu zaman kansu a shekarar 2001.

A Eritrea, ƴan jarida na fuskantar ɗauri, tare da tsarewa ba tare da shari'a ba na lokaci mai tsawo.

2. Syria

Syria dai ita ce ta biyu cikin ƙasashen da ƴan jarida ba su da cikakken ƴanci sakamakon cin zarafin da shugabannin ƙasar suka daɗe suna yi wa ƴan adawa da kafafen yaɗa labarai masu zaman kansu.

Kara karanta wannan

An ƙara yi wa dakarun sojoji sama da 20 kisan gilla a Najeriya? Gaskiya ta bayyana

A cewar ƙungiyar kare haƙƙin bil'adama ta Syria, aƙalla ƴan jarida da ma'aikatan yaɗa labarai 717 ne aka kashe a ƙasar tun shekarar 2011.

3. Afghanistan

Afghanistan ta daɗe tana shiga cikin ƙasashen da ƴan jarida ba su sakata su wala, saboda rashin tsayayyen shugabanci da rikice-rikice waɗanda suka sanya aikin jarida ke da wuya a ƙasar.

Barazana kan ƴan jarida a ƙasar na ƙara ta'azzara ne saboda rashin dokar da za ta ba su kariya da aiwatar da ita.

4. Koriya ta Arewa

Kamar ƙasar Eritrea, dukkanin kafafen yaɗa labarai a Koriya ta Arewa mallakin gwamnati ne.

Babu ƴancin ƴan jarida saboda kafafen yaɗa labarai suna yaɗa abin da kawai zai faranta ran shugaban ƙasar ne da sojoji.

5. Iran

A Iran ƴan jarida ba su da wani ƴanci sosai saboda yadda gwamnati ke kafa dokokin hana faɗar albarkacin baki da rashin aikin jarida mai zaman kansa.

Hakan ya sanya tsoro da murƙushe muryoyin masu adawa da gwamnati a ƙasar.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka mutum 8 tare da sace manajan banki a Zamfara

6. Turkmenistan

Turkmenistan, wacce ta ke a nahiyar Asia na daga cikin ƙasashen da ƴan jarida ba su da ƴanci sosai saboda yadda gwamnati ta kankame komai da hana ƴan jarida masu zaman kansu sakewa.

7. Vietnam

Rashin ƴancin jarida a Vietnam na da nasaba ne da yadda gwamnati ke iko kan kafafen yaɗa labarai, taƙaita ayyukan ƴan jarida masu zaman kansu, cin zarafin ƴan jarida da sa ido kan ayyukansu.

8. Bahrain

Ƙasar Bahrain da ke a yankin Gabas ta Tsakiya na daga cikin jerin ƙasashen da ƴan jarida ba su samun sakewa.

Ƴan jarida a lokuta da dama suna fuskantar cin zarafi da ɗauri saboda kawo rahotannin da suka caccaki gwamnati.

Fito da dokar aikin jarida ta 2002 a ƙasar ta ba da damar kulle duk wani gidan jarida da ya saɓawa gwamnati.

9. China

Ƙasar China na kula da yanayin kafofin watsa labarai ta hanyar taƙaita ayyukansu, sa ido, da kuma tsoratarwa, waɗanda dukkansu ke kawo cikas ga ƴancin ƴan jarida a ƙasar.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun hallaka mutum 2 da sace wasu da dama a Kaduna

Ƴan jarida a ƙasar na fuskantar tursasawa, sa ido, har ma da ɗauri idan suka kawo wasu rahotanni.

10. Myanmar

Myanmar na daga cikin ƙasashen da ba a sakarwa ƴan jarida mara su yi aikinsu cikin ƴanci.

Sojojin da suka yi juyin mulki a ƙasar a shekarar 2021 sun ɗauki matakan hana sakewar ƴan jarida masu zaman kansu.

Sojojin suna bibiyar ƴan jarida, kafafen yaɗa labarai inda ake ɗaure su da yi musu barazana.

An musanta harbin ɗan jarida

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Kano ta musanta zargin harsashi ya samu wani dan jarida a gidan gwamnatin jihar da ke birnin Kano.

Darakta janar na yaɗa labaran gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf, Sunusi Bature Dawakin Tofa, a wata sanarwa ya bayyana cewa babu batun harbi a fadar gwamnatin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng