Sojojin Nijar Sun Kama Hatsabibin Shugaban ’Yan Bindiga da Ya Addabi Arewacin Najeriya
- Rahotanni sun bayyana cewa sojojin kasar Nijar sun cafke wani kasurgumin dan bindigar nan na Najeriya, Kachallah Mai Daji
- An ruwaito an kama Kachallah Mai Daji a lokacin da yake yunkurin satar dabbobi a kan iyakar Najeriya da jamhuriyyar Nijar
- Kachallah Mai Daji ya shafe akalla shekara 10 yana kashe mutane, kona kauyuka, sace daruruwan mutane a Arewa maso Gabas
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Illela, Nijar - Rundunar sojin kasar Nijar ta cafke wani kasurgumin dan bindigar nan na Najeriya, Kachallah Mai Daji a kusa da garin Illela da ke kan iyaka da kasashen biyu.
Shekaru 10 na ta'addancin Kachallah
A cewar Zagazola Makama, wani mai sharhi kan harkokin tsaro, Kachallah Mai Daji ya bar aikata ta'addanci da barna a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Ya shafe akalla shekara 10 yana kashe mutane, kona kauyuka, sace daruruwan mutane da kuma ya sanya haraji a garuruwan da ya farmaka"
- A cewar Zagazola Makama.
Garuruwan da Kachallah Mai Daji ya addaba
An ce shugaban ‘yan bindigar ya fi yin ta’addanci a yankin Illela, inda ya addabi kauyuka irin su Tozai, Sabon Garin Darna, da Darna Tsolawo.
Sauran garuruwan sun hada da Tudun Gudali, Basanta, Dan Kadu, Takalmawa, Gidan Hamma, Ambarura, Gidan Bulutu da dai sauran su.
Sojojin Nijar sun kama Kachallah Mai Daji a lokacin da yake yunkurin satar dabbobi a kan iyakar Najeriya da Nijar.
A jiya Lahadi muka ruwaito cewa akalla mutane 11 suka mutu a lokacin da motoci biyu suka bi ta kadan bama-baman da 'yan bindiga suka dasa a kasa.
Lamarin ya faru ne a kananan hukumomin Gamboru-Ngala da Dikwa da ke jihar Borno.
Sojoji sun kashe 'yan bindiga a Arewa
A wani labarin kuma, Legit Hausa ta ruwaito cewa dakarun sojin saman Najeriya sun kashe 'yan bindiga da dama a wani harin sama da suka kai jihohin Borno da Neja.
Kakakin rundunar NAF, AVM Edward Gabkwet ya kuma bayyana cewa dakarun rundunar sun kai samame yankin Neja-Delta inda suka dakile barayin mai da masu fasa bututun man.
Asali: Legit.ng