Kura ta ci kura: An yi artabu tsakanin kungiyoyin 'yan bindiga biyu a jihar Katsina

Kura ta ci kura: An yi artabu tsakanin kungiyoyin 'yan bindiga biyu a jihar Katsina

- Kaikayi ya koma kan mashekiya a dajin kauen Illela da ke yankin karamar hukumar Safana a jihar Katsina

- 'Yan bindiga kimanin dari uku, a karkashin kungiyoyi uku, sun gwabza kazamin rikici a tsakaninsu

- Rahotannin sun bayyana cewa fiye da mutum dari daga cikin 'yan bindigar sun rasa rayukansu yayin rikicin a ranar Alhamis

Wasu kungiyoyin 'yan bindiga guda biyu da ke adawa da juna sun gwabza kazamin rikici a yankin kauyen Illela da ke yankin karamar hukumar Safana a jihar Katsina, kamar yadda rahoton HumAngle, wanda ya samo asali daga Daily Trust, ya nuna.

Rahoton Daily Trust ya bayyana cewa an fafata rikicin ne a tsakanin yaran Mani Sarki da yaran Dankarami wadanda suka samu goyon bayan Abu Rada. Dukkaninsu shugabannin kungiyoyin ta'addanci ne da suka addabi Safana da kewaye.

Wasu shaidun gani da ido sun shaidawa Daily Trust cewa an samu asarar rayuka yayin da wasu da dama daga cikin 'yan ta'addar suka samu raunuka.

Shaidun sun bayyana cewa tawagar 'yan ta'adda ta kai wa Mani Sarki hari duk da ya yi hijira daga yankinsa zuwa dajin Illela bayan ya kulla yarjejeniyar zaman lafiya da gwamnatin jihar Katsina.

KARANTA: Babban sarkin kabilar Yoruba ya aika muhimmin sako ga 'yan siyasa bayan ganawa da Buhari

Sai dai, kungiyoyin 'yan bindiga da dama basu ji dadin kulla yarjejeniyar zaman lafiyar ba, lamarin da yasa wata tawaga a karkashin Dan Da da ke karkashin Alhaji Dankarami ta kai wa Mani Sarki hari a Illela.

Kura ta ci kura: An yi artabu tsakanin kungiyoyin 'yan bindiga biyu a jihar Katsina
Kura ta ci kura: An yi artabu tsakanin kungiyoyin 'yan bindiga biyu a jihar Katsina
Asali: Twitter

Wata majiyar ta bayyana cewa rikicin ya samo asali ne tun a baya; lokacin da wani kani wurin Mani Sarki ya karbi N500,000 a matsayin kudin fansa bayan ya yi garkuwa da matar wani dan bindiga da ke sansanin Dangwate.

KARANTA: Zamfara: 'Yan bindiga sun kai hari mazabar shugaban majalisa, sun hallaka mutane uku

A cewar rahoton Daily Trust, tun a can baya, an kashe kanin Mani Sarki wanda ake kira da suna 'Chirwa' da matarsa yayin da wasu 'yan ta'adda uku - Kabiru, Tanimu, da Sulaiman - suka samu raunuka kuma suke samun kulawa a wani asibitin Katsina.

An samu mabanbantan ruwayoyi dangane da silar barkewar rikicin. Wasu sun ce an samu sabani a tsakanin kungiyoyin 'yan ta'addar akan shirin mika wuya ga hukuma ta hanyar sulhu.

A cewar wata majiyar, kimanin 'yan bindiga 300 ne ake zargin suna cikin jejin a lokacin da suke fafata rikici da juna kuma fiye da 100 sun mutu yayin rikicin.

Rahotanni sun bayyana cewa jami'an tsaro sun janye jikinsu tare da barin 'yan bindigar su ci kansu - kura ta ci kura - tunda rikicin a tsakaninsu ne, kuma dukkansu makiyan kasa da jama'a ne.

A kwanakin baya Legit.ng ta rawaito shugaban kasa, Muhammadu Buhari, na cewa ko kadan ba ya jin dadin yadda 'yan ta'adda ke salwantar da rayukan jama'a a sassan Nigeria.

A cewar Buhari, gwamnatinsa ta yi wasu tsare-tsare domin kawo karshen kungiyar Boko haram a cikin shekarar 2021.

Buhari ya lissafa wasu jiga-jigan dalilai guda hudu da zasu bawa gwamnatinsa damar ganin bayan kungiyar Boko Haram da sauran kungiyoyin 'yan ta'adda a cikin wannan shekarar, 2021.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng