Gwamnati Ta Fara Raba Tallafin N50, 000, ’Yan Najeriya Miliyan 1 Za Su Amfana

Gwamnati Ta Fara Raba Tallafin N50, 000, ’Yan Najeriya Miliyan 1 Za Su Amfana

  • Gwamnati ta ce ta fara raba tallafin N50,000 ga 'yan Najeriya miliyan 1 da suka samu shiga shirin tallafawa kanananun 'yan kasuwa
  • Ministar masana'antu, kasuwanci da zuba jari, Dr Doris Uzoka-Anite, ta ce akalla mutane 200,000 sun samu tallafin zuwa yanzu
  • Uzoka-Anite daga nan zuwa karshen watan Mayu, sauran mutane 800,000 za su karbi kudadensu yayin da aka ware masu N50bn

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Wadanda za su ci gajiyar tallafin N50,000 da gwamnatin tarayya za ta rabawa kananun 'yan kasuwa sun fara karbar kudaden su.

Gwamnatin tarayya ta fara raba tallafin N50bn ga 'yan Najeriya
Gwamnati ta fara raba N50,000 ga mutane miliyan 1, zuwa yanzu mutum 200,000 sun samu tallafin. Hoto: @officialABAT, @DrDorisAnite
Asali: Facebook

Ministar masana'antu, kasuwanci da zuba jari, Dr Doris Uzoka-Anite, wadda ta tabbatar da hakan a karshen mako, ta ce akalla kananan 'yan kasuwa 200,000 ne suka karbi kudin.

Kara karanta wannan

Zargin N70b: Wasu 'yan Arewa sun goyi bayan Ministan tsaro, Bello Matawalle

Za a raba N50bn ga mutane miliyan

A cewar ministar, wasu kanananun 'yan kasuwa 800,000 za su samu tallafin kudin kafin a rufe shirin nan da ranar 31 ga watan Mayu, in ji rahoton jaridar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan zai kawo adadin wadanda za su ci gajiyar tallafin ga ‘yan Najeriya 1,000,000 da suka fito daga kananan hukumomi 774, kamar yadda gwamnati ta tsara.

Ta bayyana cewa kimanin mutane miliyan 3.6 ne suka nemi tallafin inda aka zabi mutane miliyan 1 da za su amfana da bayan cika dukkanin ka'idoji.

Ministar ta ce an ware Naira biliyan 50 a cikin kasafin kudin 2024 domin rabawa wadanda suka samu shiga cikin shirin.

Gwamnati za ta tallafawa 'yan kasuwa

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa shirin na daya daga cikin matakan rage wa 'yan Najeriya radadi da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya aiwatar bayan janye tallafin man fetur.

Kara karanta wannan

A tuna da matattu: Sanata a Kano ya rabawa 'yan mazabarsa likkafani da tukwanen kasa

Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta mayar da hankali wajen bunkasa kananun 'yan kasuwa wadanda ya ke ganin za su fi saurin kawo sauyi a rayuwar 'yan kasar.

Hakazalika shugaban ya kuma ce za a ba kamfanonin sarrafa kayayyaki 75 rancen kudi har Naira biliyan 1 ga kowannensu domin daidaita kasuwancinsu.

Gwamnati ta takaita kai wuta waje

A wani labarin kuma, gwamnatin tarayya ta sanar da cewa ta takaita kai wutar lantarki zuwa kasashen waje a wani yunkuri na daidaita samuwar wutar a cikin gida.

Daga cikin kasashen da wannan dokar ta shafa akwai Jamhuriyar Nijar, Togo da Mali, wadanda Najeriya ke bin bashin kudin wuta da ya hauwa Naira biliyan 130.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.