"Yadda Aka Sace Takardar da Marigayi Yar'adua Ya Rubuta Lokacin Jinya a Saudiyya"
- Sanata Abdul'aziz Yar'adua ya bayyana yadda aka ɓatar da takardar miƙa mulki da marigayi Umaru Musa Yar'adua ya rubuta lokacin yana jinya
- Ƙanin tsohon shugaban ƙasar ya ce ya shiga damuwa lokacin da mutane suka fara surutu amma da ya bincika sai ya gano inda matsalar take
- Ya yi wannan bayanin ne a wurin taron tunawa da marigayin wanda gwamnatin jihar Katsina ta shirya ranar Lahadi
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Katsina - A ranar Lahadi, 5 ga watan Mayu, 2024 ne marigayi tsohon shugaban ƙasa, Alhaji Umaru Musa Yar'adua ya cika shekara 14 da rasuwa.
Tun gabanin rasuwarsa, mutane sun yi ta ƙorafin cewa duk da yana fama da jinya marigayin bai miƙa mulki ga mataimakinsa, Goodluck Jonathan ba a wancan lokacin.
Ƙanin marigayi tsohon shugaban ƙasar kuma sanatan Katsina ta Tsakiya, Abdulaziz Yar’adua, ya bayyana cewa yayansa ya rubuta takardar miƙa mulki ga Jonathan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda takardar Ummaru Yar'adua ta ɓace
Kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito, Sanatan ya ce lokacin da rashin lafiyar marigayi Ƴar'adua ta yi tsanani, ya rubuta takardar miƙa mulki ga Jonathan amma wasu bara gurbi suka sace ta.
Sanata Abdulaziz Yar’Adua ya faɗi haka ne a wurin taron addu'o'in tunawa da tsohon shugaban ƙasar wanda ya gudana a gidan gwamnatin jihar Katsina, rahoton Daily Trust.
Sanata ‘Yar’adua ya ce a lokacin yana kasar Saudiyya yayin da marigayi shugaban kasar ke cikin mawuyacin hali, ya ji mutane na korafin cewa dan uwansa bai mika mulki ba.
Ya ƙara da cewa:
"Na shiga damuwa sosai kan raɗe-raɗin ya bar Najeriya ba tare da miƙa mulki ba musamman saboda ni na san halinsa. Amma da na bincika sai na gano ya rubuta takardar (miƙa mulkin) amma ba a kai ta inda ya dace ba.
"Wannan dalilin ne ya sa aka yi amfani da umarnin doka na abin da ya shafi lalura a wancan lokacin."
Sanatan ya godewa gwamnatin Katsina bisa shirya taron tunawa da ayyukan alherin da Marigayi ‘Yar’adua ya yi, wadanda a cewarsa sun yi matukar tasiri ga jihar da kasa baki daya.
Tsohon kwamishina ya rasu a Taraba
A wani rahoton kun ji cewa an shiga jimami a jihar Taraba bayan mutuwar tsohon kwamishinan lafiya a gwamnatin Injiniya Darius Ishaku
Marigayin mai suna Dakta Innocent Vakkai ya rasu ne a ranar Juma'a 3 ga watan Mayu a babban asibitin Tarayya a Jalingo
Asali: Legit.ng