Harin Jangebe: Ganduje ya bada umurnin rufe makarantun kwana 10 a Kano

Harin Jangebe: Ganduje ya bada umurnin rufe makarantun kwana 10 a Kano

- Gwamnatin jihar Kano ta bada umurnin rufe makarantun kwana guda 10 a sassan jihar

- Gwamnatin ta dauki wannan matakin ne don kare lafiyar yara duba da sace yara da ake yi a jihohin da ke makwabtaka da ita

- Kwamishinan Ilimi na Kano ya ce iyayen yara da abin ua shafa su tafi su kwashe yaransu har zuwa nan gaba da za a sanar da bude makarantun

Gwamnatin jihar Kano ta sanar da rufe makarantun kwana 10 a sassan jihar nan take biyo bayan sace yan matan makarantar GGSS Jangebe a jihar Zamfara, Daily Trust ta ruwaito.

Kwamishinan Ilimi na jihar, Muhammad Kiru ya ce gwamnatin ta cimma matsayin ne bayan nazari da bita kan abubuwan da ke faruwa a jihohin da ke makawabtaka da ita inda ake sace dalibai.

Harin Jangebe: Ganduje ya bada umurnin rufe makarantun kwana 10 a Kano
Harin Jangebe: Ganduje ya bada umurnin rufe makarantun kwana 10 a Kano. Hoto: @daily_trust
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Harsashin bindiga ba zai magance yan bindiga ba, Adamu Garba

A cewarsa, rashin tsaron ne ya tilastawa gwamnatin daukar matakin domin kare lafiya yaran.

Ya ce iyaye da masu kulawa da yara su tafi su kwashe yaransu daga makarantun, nan gaba gwamnati za ta sanar da ranar da za a bude makarantun don cigaba da karatu.

Ya lissafa makarantun da abin ya shafa kamar haka: Maitama Sule Science College, Gaya; Boarding Secondary School, Ajingi; Girls Secondary Schools a Sumaila, Gezawa da Jogana, Kachako da wani a Unguwar Gyartai a Kunchi da kuma Girls Secondary School, Albasu.

KU KARANTA: Sheikh Ahmad Gumi ya yi martani kan sace ƴan matan makarantan Zamfara

Sauran sun hada da Makarantar Sakandare ta maza da ke Maiyaki da Unity College a Karaye.

A wani labarin daban, ofishin mai bawa Shugaban Kasa shawara kan Tsaro da Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Isa Ali Pantami, a jiya sun sha banban kan kaddamar da fasahar sadarwa ta 5G a Najeriya, Daily Trust ta ruwaito.

Sun yi magana ne a Abuja yayin wani taro da kwamitocin Majalisar Dattawa kan Sadarwa, Kimiyya da Fasaha, da Yaki da Laifukan Yanar Gizo da Lafiya da Cututtuka masu Yaduwa suka shirya kan matsayin fasahar 5G.

A yayin da Pantami ya ce Najeriya ta shirya tsaf domin kaddamar da fasahar 5G, ofishin NSA ta nuna damuwarta kan wasu matsaloli da ke tattare da fasahar.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel