Kwanaki Kusan 7 da Kammala Taro a Kasar Saudi, Shugaba Tinubu bai Dawo Najeriya ba

Kwanaki Kusan 7 da Kammala Taro a Kasar Saudi, Shugaba Tinubu bai Dawo Najeriya ba

  • Bola Ahmed Tinubu ya bar Najeriya tun kwanaki, har yau jirginsa bai dawo gida ba, hakan ya sa aka fara maganganu
  • Fadar shugaban kasa ba tayi wa jama’a bayanin inda shugaban Najeriyan ya shiga bayan kama taro a kasar Saudi ba
  • Ana sa ran Bola Ahmed Tinubu ya dawo Abuja a yau, wasu sun fara tunanin shugaban kasar ya ziyarci likitocinsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Jama’a sun fara jefo alamar tambaya ta ko ina ganin har yanzu Mai girma Bola Ahmed Tinubu bai dawo gida watau Najeriya ba.

Kwanaki shida da suka gabata aka kammala taron WEF na tattalin arzikin duniya a birnin Riyadh a Saudi wanda Bola Ahmed Tinubu ya halarta.

Kara karanta wannan

"Ya kware a cin amana": APC ta ja kunnen Tinubu kan sake jiki da gwamnan PDP

Bola Tinubu
Shugaba Bola Tinubu bai dawo Najeriya daga kasar Saudi ba Hoto: @DolusegunX
Asali: UGC

Ina shugaba Bola Tinubu ya shiga?

Daily Trust ta rahoto cewa har yanzu babu wanda ya san inda shugaban Najeriya ya shiga, kusan mako guda kenan babu wata duriyarsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ranar Litinin aka gama zaman da aka yi a kasar Saudi Arabiya, tun lokacin ake tsammanin ganin jirgin shugaban Najeriya a Abuja.

Tinubu: Fadar shugaban kasa ta yi gum

Kwanaki shida kenan Bola Tinubu bai dawo bakin aiki ba, kuma babu jawabin da aka fitar game da tafiyar daga fadar shuagaban kasa.

Sahara Reporters ta ce jirgin kasuwa aka yi haya domin daukar shugaba Tinubu zuwa Saudi, har yau kuma babu labarin inda ya shige.

Hadimai ba su maganar ina Tinubu yake

Legit ta duba shafin mai taimakawa shugaban Najeriyan a kafafen sada zumunta na zamani, Olusegun Dada domin jin inda akwa kwana.

Kara karanta wannan

Badakalar N80bn: Abin da wasu tsofaffin gwamnoni ke cewa game da Yahaya Bello

A shafinsa na X, Olusegun Dada bai yi maganar lokacin da Bola Tinubu zai dawo ba.

Abin da mu ka ci karo da shi bai wuce jawabi na musamman da shugaban kasar ya fitar, yana taya Simon Lalong murnar cika shekara 61.

Shugaban kasa Tinubu ya tafi asibiti ne?

Rahotonni sun ce wannan shiru ya jawo an fara tunanin ko Tinubu ya tafi Faransa domin ya saba zuwa ganin likitocinsa a birnin Faris.

Wata majiya ta shaidawa jaridar cewa bayan gama taron Riyadh, Tinubu ya wuce Landan domin wata ziyara da ba ta alaka da aikin ofis.

An kara albashin majalisa a mulkin Tinubu?

Rahoto ya zo cewa ana rade-radin cewa gwamnatin tarayya ta yi wa Sanatoci da 'Yan majalisa karin albashi a lokacin matsin tattali.

Ja'afar Ja’afar ya yi ikirarin Sanatoci masu karbar N13m sun koma tashi da N21m, kudin ‘yan majalisa ya karu zuwa N13m a duk wata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng