Binciken Matawalle: An Yi Sabuwar Fallasa Kan Masu Zanga-Zanga a EFCC

Binciken Matawalle: An Yi Sabuwar Fallasa Kan Masu Zanga-Zanga a EFCC

  • Ƙungiyar matasan jam'iyyar APC a jihar Zamfara ta nesanra kanta daga masu zanga-zangar neman a binciki tsohon gwamnan jihar Bello Matawalle
  • Shugaban ƙungiyar a wata sanarwa ya yi fatali da zarge-zargen da ake yi wa ƙaramin ministan tsaron kan karkatar da kuɗaɗen Zamfara
  • Ya ƙalubalanci waɗanda suka ɗauki nauyin zanga-zangar da su kawo shaidar da ke nuna cewa Matawalle ya yi almundahana da dukiyar jihar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Ƙungiyar matasan jam’iyyar APC ta Zamfara ta ce ba ta cikin masu neman a binciki Bello Matawalle, tsohon gwamnan jihar.

A ranar 3 ga watan Mayu, wata ƙungiya da aka bayyana a matsayin APC Akida ta yi zanga-zanga a hedkwatar hukumar EFCC da ke Abuja, inda ta buƙaci a sake buɗe ɓinciken da ake yi wa tsohon gwamnan kan badaƙalar N70bn.

Kara karanta wannan

Gwamnan Sokoto ya shirya samarwa matasa aikin yi, ya yi wata hubbasa

An caccaki masu son a binciki Matawalle
Matasan APC sun caccaki masu zanga-zangar neman a binciki Bello Matawalle Hoto: Dr. Bello Matawalle
Asali: Facebook

A wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, shugaban ƙungiyar matasan APC na Zamfara, Abubakar Gusau, ya ce masu zanga-zangar na da nasaba da siyasa domin ɓata sunan Matawalle da mutuncinsa, cewar rahoton jaridar The Cable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abubakar Gusau ya yi watsi da zarge-zargen da ake yi wa ƙaramin ministan tsaron, inda ya ce Matawalle ya bi tsarin da ya dace kan kowace kwangilar da ya bayar kuma an aiwatar da dukkan ayyukan, rahoton Tribune ya tabbatar.

Me suka ce kan binciken Matawalle?

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Babu wata takardar shaida inda aka tuhumi tsohon gwamnan da laifin almubazzaranci da karkatar da dukiyar al’umma domin azurta kansa."
"Bugu da ƙari, babu wani kwamitin binciken shari’a ko hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa a jihar Zamfara da ya tuhumi Bello Matawalle da laifin almundahana."

Kara karanta wannan

Gwamna Dikko Radda ya fadi dalilin gwamnonin Arewa na yin taro a Amurka kan tsaro

"Abu mafi mahimmanci shi ne, akwai hukuncin da kotu ta yanke wanda ya hana EFCC bincike, kamawa, da gurfanar da Matawalle. Har yanzu wata babbar kotu ba ta janye wannan hukuncin ba.
"Muna ƙalubalantar wadanda suka ɗauki nauyin wannan zanga-zangar da su ba al’umma duk wata shaida da ke nuna cewa Matawalle ya karɓi kuɗi daga hannun wani ɗan kwangila a matsayin cin hanci lokacin da yake kan mulki ko su nuna wani asusu na banki da ya tara irin waɗannan kuɗade."

Batun binciken Matawalle

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar EFCC ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da gudanar da bincike kan zargin almundahanar Naira biliyan 70 da ake yi wa Bello Matawalle.

Hukumar ta bayar da wannan tabbacin ne ga masu zanga-zangar da suka je hedkwatarta da ke Abuja domin neman a sake buɗe binciken tsohon gwamnan na jihar Zamfara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng