"A bi Tsarin Hisbah": Shekarau Ya Shawarci Tinubu Kan 'Yan Sandan Jihohi, Ya Yi Gargadi

"A bi Tsarin Hisbah": Shekarau Ya Shawarci Tinubu Kan 'Yan Sandan Jihohi, Ya Yi Gargadi

  • Sanata Ibrahim Shekarau ya ba Gwamnatin Tarayya shawara kan kirkirar 'yan sandan jihohi a fadin Najeriya baki daya
  • Shekarau ya ce ya kamata a hana jami'an rike manyan makamai domin gudun dawo da 'yan daban siyasa a jihohi
  • Ya shawarci yin amfani da 'yan sandan a jihohi kamar yadda ya yi ga hukumar Hisbah a lokacin da ya ke mulki a Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Tsohon gwamnan jihar Kano, Mallam Ibrahim Shekarau ya shawarci Shugaba Bola Tinubu kan 'yan sandan jihohi.

Shekarau ya shawarci gwamnatin kan hana 'yan sandan riƙe makamai bayan tabbatar da su domin dakile abin zai je ya dawo.

Kara karanta wannan

"Jama'a sun ƙosa a yanzu": Sarkin Musulmi ya kuma jan hankalin shugabanni

Shekarau ya ba Tinubu shawara kan 'yan sandan jihohi
Sanata Ibrahim Shekarau ya shawarci Bola Tinubu inda ya ce bai kamata a ba 'yan sandan jihohi makamai ba. Hoto: @MallamShekarau, @officialABAT.
Asali: Twitter

Wasu matsaloli Shekarau ya hango?

Sanatan ya nuna damuwa inda ya ce idan aka tabbatar da 'yan sandan ba tare da tsari ba, hakan zai kara yawaitar 'yan daban siyasa a jihohi da dama.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Duk da ya goyi bayan ƙirƙirar 'yan sandan amma ya yi gargadi kan barin jami'an su rike muggan makamai a tare da su, Tribune ta tattaro.

Ya ce mafi yawanci 'yan siyasa ne ke daukar nauyin duk wani ta'addanci na siyasa a jihohinsu, cewar The Nation.

Shekarau ya nemo mafita kan 'yan sandan

Tsohon ministan ya bukaci yin tsar kamar hukumar Hisbah wanda ya yi amfani da su wurin dakile laifuffukan al'umma lokacin da ya ke mulkin Kano.

Wannan na zuwa ne bayan shugaban kasa da gwamnoni 36 sun amince da ƙirƙirar 'yan sanda jihohi domin inganta tsaro a ƙasar.

Kara karanta wannan

Borno: Gwamna Zulum ya tafka babban rashi yayin da hadiminsa ya rasu

Wasu da dama sun goyi bayan tsarin ƙirƙirar 'yan sandan sai dai masu ruwa da tsaki sun kushe yunkurin inda suke zargin gwamnonin za su yi amfani da su ta hanyar da bai dace ba.

An sake maka Ganduje a kotu

A wani labarin, wani tsohon mai neman takarar kujerar APC a Najeriya, Mohammed Saidu-Etsu ya maka shugaban APC, Abdullahi Ganduje a kotu.

Etsu ya na kalubalantar sahihancin shugabancin Ganduje ne inda ya ce bai kamata a nada shi a muƙamin ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.