Gwamna Dikko Radda Ya Fadi Dalilin Gwamnonin Arewa Na Yin Taro a Amurka Kan Tsaro
- Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya kare taron da wasu gwamnonin Arewacin Najeriya suka halarta a Amurka kan tsaro
- Gwamnan ya bayyana cewa gayyatarsu aka yi taron domin nemo hanyoyin da za a magance matsalar rashin tsaro da addabi yankin
- A cewar gwamnan taron ya ba su damar fahimtar ƙalubalen rashin tsaro da ya daɗe yana ci wa yankin tuwo a ƙwarya
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Katsina - Gwamna Dikko Umaru Radda na jihar Katsina ya kare ziyarar da gwamnonin Arewa suka kai ƙasar Amurka.
Gwamnan ya ce sun yi hakan ne domin nemo mafita mai ɗorewa kan matsalar rashin tsaro da ke addabar yankin.
Gwamnonin dai sun sha suka kan ziyarar da suka kai Amurka. Sai dai, Radda ya ce ziyarar wani bangare ne na ɗaukar matakan magance matsalar tsaro a Arewacin ƙasar, inda ya bayyana cewa gayyatarsu aka yi taron.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Radda ya kare matakinsu na zuwa Amurk ne a wata tattaunawa da tashar Channels tv a shirinsu na 'Politics Today' a ranar Juma'a.
Meyasa suka halarci taron?
"Gwamnoni 10 sun je birnin Washington D.C a Amurka, kuma mun yi taron tattaunawa da cibiyar zaman lafiya ta Amurka domin mu samar da hanyoyin da za su kawo ƙarshen rashin tsaro da ke damun jama’armu."
"Dukkaninmu mun zauna na kwanaki sannan mun yi nasarar yin musayar ra'ayoyi tare da tattaunawa da masu ruwa da tsaki da ke da hannu wajen kawo zaman lafiya da tsaro mai ɗorewa a duniya."
- Dikko Umaru Radda
Gwamna Radda ya fadi dalilinsu
Duk da sukar da ake yi kan taron tare da tambayar dalilin da ya sa aka gudanar da taron a Amurka ba a Najeriya ba, Gwamna Radda ya kare matakinsu na halartar taron.
A kalamansa:
"Taron ba wai gwamnonin da aka zaɓa suka shirya shi ba, amma cibiyar zaman lafiya ta Amurka ce ta shirya shi. Su ne suka gayyace mu sannan muka yi taron da su."
"An gayyyace mu ne domin mu zauna da su ta yadda za mu samo mafita mai ɗorewa kan matsalolim da suka addabi al'ummar mu."
A cewar Radda, ziyarar ta Amurka ta ba gwamnonin damar fahimtar ƙalubalen tsaron da ke addabar yankin Arewa.
An caccaki gwamnonin Arewa
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ya caccaki gwamnonin Arewa kan tafiyar da suka yi zuwa ƙasar Amurka.
Sule Lamido ya ce ziyarar da gwamnonin Arewa suka kai Amurka ta fallasa jahilcinsu ga kundin tsarin mulkin Tarayyar Najeriya.
Asali: Legit.ng